Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun sake farmakar jihar Kaduna, sun yi mummunan aika-aikata

Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun sake farmakar jihar Kaduna, sun yi mummunan aika-aikata

  • Wani sabon harin 'yan bindiga a Kaduna yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama a yau Lahadi inji majiyoyi
  • Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan sace wasu mutane a jajibirin Kirsimeti da aka gudanar na shekarar 2021
  • Kawo yanzu, ba a tabbatar da faruwar lamarin a hukumance ba, amma jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sanda ya ce zai yi bayani

Kaduna - Wasu ‘yan bindiga sun sake kashe wasu mutanen kauyuka biyar tare da yin garkuwa da wasu 16 a kauyen Kerawa da ke karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna.

Wannan lamari ya faru ne da safiyar yau Lahadi lokacin da ‘yan bindigar suka mamaye kauyen.

Taswirar jihar Kaduna
Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun sake hallaka mutane a Kaduna, sun sace 16 | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

‘Yan bindiga a baya sun sace mutane 12 wadanda daga cikinsu 10 mata ne a kauyen a jajibirin Kirsimeti.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Yan bindiga sun sun yi awon gaba da matan aure da yan mata a sabon harin jihar Kaduna

Wani tsohon kansilan yankin, Daiyabu Kerawa, wanda ya tabbatar wa Daily Trust faruwar lamarin, ya ce mazauna kauyen sun fice dag kauyen bayan harin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Babu wani martani a hukumance daga gwamnatin jihar amma jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Jalige Mohammed, ya yi alkawarin samar da cikakken bayani kan lamarin.

Wasu bayanai guda biyu da kwamishinan tsaro na cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya bayar a ranar Lahadin da ta gabata sun tabbatar da kisan da wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka yi.

Ya ce jami’an tsaro sun kai wa gwamnatin jihar Kaduna rahoton cewa mutane hudu sun mutu, daya kuma ya jikkata, a wani hari da ‘yan bindiga suka kai a Kerawa, karamar hukumar Igabi, kamar yadda Daily Nigerian ta rahoto.

Kara karanta wannan

‘Yan sanda sun kai samame sansanin ‘yan bindiga a Kaduna, sun ceto mutum 9

A cewar sanarwar Aruwan game da rahoton 'yan sanda:

“A cewar rahoton, ‘yan bindiga sun kai hari kauyen, inda suka yi ta harbe-harbe, sannan suka kashe mazauna garin hudu, Lado Shuaibu, Usman Haruna, Ayuba Muntari da Jafar Abdullahi.
“An bar Mallam Mamuda da rauni, yayin da ‘yan bindigar suka kwashe wasu babura da kayayyaki daga al’umma."

An samu wasu munanan hare-hare daban-daban a jihar a cikin 'yan kwanakin nan.

Yan bindiga sun bindige Jigon APC har lahira jim kadan bayan ya kammala addu'o'i

A wani labarin, jigon jam'iyyar APC, Mista Otu Inyang, ya rasa rayuwarsa bayan wasu yan bindiga sun bude masa wuta a kauyen Ikot Udoma, karamar hukumar Iket, jihar Akwa Ibom.

Daily Trust ta rahoto cewa maharan sun bindige shi ne jim kadan bayan ya kammala addu'o'in sabuwar shekara a coci.

Rahoto yace Yan bindigan sun bibiyi Jigon APC a jihar suka harbe shi mintuna kadan kafin shigar sabuwar shekara yayin da yake kan hanyar koma wa gida bayan halartan addu'o'i a cocin Qua Iboe.

Kara karanta wannan

An kama masu garkuwa da mutane yayin da suke jiran kudin fansar wadanda suka sace a Katsina

Asali: Legit.ng

Online view pixel