Bayan neman sulhu, shugaban 'yan bindiga,Turji, ya sako mutum 52 da ya yi garkuwa da su

Bayan neman sulhu, shugaban 'yan bindiga,Turji, ya sako mutum 52 da ya yi garkuwa da su

  • Shugaban 'yan bindiga kuma gagararre, Bello Turji, ya sako mutane 52 da yayi garkuwa da su a karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara
  • A halin yanzu, motoci sun yi jeri suna jiran mutane 52 domin a kusa da hanyar Maberiya da ke Shinkafi domin karbar wadanda aka sako
  • Wannan al'amari ya na daga cikin matakan da Turji ya fara dauka bayan aikewa da wasikar neman sasancin da yayi wa masarautar Shinkafi a watan da ya gabata

Zamfara - Bello Turji, gagararren dan bindigan jihar Zamfara, a ranar Litinin ya sako mutane 52 wadanda suka dade a hannunsa, wata majiya ta tabbatar wa da Daily Trust hakan.

"Wadanda aka sako din a halin yanzu ana fito da su daga daji zuwa wani wuri da aka yi yarjejeniya inda daga nan za a kai su garin Shinkafi.

Bayan neman sulhu, shugaban 'yan bindiga,Turji, ya sako mutum 52 da ya yi garkuwa da su
Bayan neman sulhu, shugaban 'yan bindiga,Turji, ya sako mutum 52 da ya yi garkuwa da su
Asali: Original
"Motoci sun yi layi kuma an umarce su da su fara tafiya hanyar Maberiya, wani yanki da ke da nisan kilomita 5 daga gabashin garin Shinkafi," wani mazaunin yankin da ya bukaci a bye sunansa ya sanar.

Turji shi ne mai shirya kashe-kashe da satar mutane a Shinkafi da kewaye zuwa kananan hukumomin Sabon Birni da Isah a jihohin Zamfara da Sokoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daily Trust ta ruwaito cewa, a watan da ya gabata, Turji ya rubuta wasika ga masarautar Shinkafi inda ya jaddada shirinsa na ajiye makamai da rungumar zaman lafiya.

Majiyoyi sun ce ya na daga cikin batun sasancin ne lamarin da yasa Turji ya sako wadanda aka sace.

Zamfara: Yadda luguden jiragen NAF ya yi ajalin shugabannin 'yan bindiga da wasu

A wani labari na daban, luguden wutar jiragen saman sojin sama na Najeriya a sa'o'in farko na ranar Asabar ya yi ajalin rayukan shugabannin 'yan bindiga biyu da wasu miyagun 'yan ta'adda da ke addabar jama'a a karamar hukumar Birnin Magaji ta jihar Zamfara.

Daily Trust a ranar Lahadi ta tattaro cewa, gagararren dan bindiga, Alhaji Auta, ya sheka lahira bayan bam din da jirgin sojoji ya wurga ya tashi da shi yayin da ya ke kan babur tare da shanunsa daga sansaninsu.

Farmakin ya lamushe rayukan wasu 'yan kungiyarsa da ke kusa da sansani da kuma wadanda ke yankin, Daily Trust ta ruwaito.

Samamen da aka kai sansanin Auta ya na daga cikin manyan nasarori da sojin saman Najeriya suna samu, bayan farmakin da ya yi ajalin shugabannin 'yan bindiga Tawaye a Dumburm a makon farko na Disamba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel