Ba dani ba: Lauyan Sunday Igboho ya zare hannunsa a rikicinsu da gwamnatin Buhari

Ba dani ba: Lauyan Sunday Igboho ya zare hannunsa a rikicinsu da gwamnatin Buhari

  • Lauyan Sunday Igboho ya ce ya zare hannunsa a batun da yake da alaka da Sunday Igboho da gwamnatin Najeriya
  • Ya ce ya gamsu da jin dadin yadda tawagarsu tayi kokarin wajen kare hakkin Sunday Igboho da 'yan tsaginsa
  • Hakazalika, ya ce bayyana karara cewa, shi sam bai da hannu a kowane aiki da yake da alaka da awaren Yarbawa

Lauya Pelumi Olajengbesi, daya daga cikin lauyoyin da ke kare Sunday Adeyemo, shugaban 'yan awaren Yarbawa wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya yi murabus daga tawagar kare dan awaren.

Idan baku manta ba, a baya mun kawo muku rahotannin yadda gwamnatin jamhuriyar Benin ta kame Sunday Igboho ta tasa keyarsa magarkama a kasar.

Daga nan ne batutuwa suka fara girma, gwamnatin Najeriya ta fara bibiyar yadda za ta dawo dashi Najeriya don gurfanar dashi.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta san abun yi don kawo karshen rashin tsaro cikin watanni 17 – Gwamnan APC

Dan faftukar kafa kasar Yarbawa, Sunday Igboho
Ba dani ba: Lauyan Sunday Igboho ya zare hannunsa a shari'arsa da gwamnatin Buhari | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Olajengbesi ya sanar da murabus din nasa ne a ranar Lahadi 2 ga watan Janairun 2022 a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook.

Lauyan ya ce ya gamsu da irin gudunmawar da yake baiwa tawagar lauyoyin, inda ya ce ba ya son a sake hada shi da duk wara kungiyar aware a kasar musamman ta Yarbawa.

Sanarwar ta kara da cewa:

"Wannan kenan don in sanar da murabus dina a hukumance a matsayin lauya da bin duk wani lamari da ya shafi Cif Sunday Adeyemo Igboho da kuma 'yan awaren Yarbawa."
“A matsayinmu na kamfani, mun gamsu da mafi kwarewar mu na bayar da gudunmawar samar da mafita da wakilci na shari’a ga Igboho da sauran masu fafutuka na Yarbawa wajen tabbatar da kariya da kuma kwato musu hakkinsu a wannan lamarin.

Kara karanta wannan

Ba yaƙi na ke yi da Buhari ba, Sunday Igboho ya fitar da saƙon sabuwar shekara

“Mun samu nasarar sako wasu mutane 12 da jami’an tsaron farin kaya (SSS) suka kama bisa zalunci, kuma mun samu nasarar sakin wani dan gargajiya da ba shi da laifi, kamar dai yadda jami’an SSS suka kama da kuma tsare su ba bisa ka’ida ba.
“Na bayyana tun farko cewa aikina zai kasance ne kawai a cikin kwarewa ta a matsayina na lauyan Sunday Igboho da 'yan koronsa.
"Ni mai cikakken imani ne ga tsarin mulkin dimokuradiyya, 'yancin walwala da 'yancin dan adam wanda ya hada da 'yancin cin gashin kai amma ni ba dan aware bane na kasar Yarbawa ko kuma memba na wata kungiya."

Murabus din Olajengbesi na zuwa ne kwanaki bayan Banji Akintoye, shugaban kungiyar Ilana Omo Oodua Worldwide, wata kungiyar Yarbawa mai cin gashin kanta, ya ce nan ba da jimawa ba za a sako Igboho daga tsare shi da ake.

Kotu Ta Tura Sunday Igboho Gidan Yari a Kwatano

Kara karanta wannan

Kasa da sa'o'i 10 da aure, ango ya masgi amarya, ta tsere ta bar shi tare da kashe auren

A tun farko, Kotun Jamhuriyar Benin da ke zamanta a Kwatano ta tura Sunday Adeyemo da aka fi sani da Sunday Igboho zuwa gidan yari, The Cable ta ruwaito.

An kammala zaman kotun ne misalin ƙarfe 11.20 na daren ranar Litinin bayan shafe kimanin awanni 13.

Wani majiya daga kotun ta shaidawa The Cable cewa ba za a saki Igboho ba. "Matsalar mayar da wanda ake zargin da laifi ƙasarsa domin ya fuskanci sharia lamari ne da akwai siyasa sosai a cikinsa."

Asali: Legit.ng

Online view pixel