Zamfara: Yadda luguden jiragen NAF ya yi ajalin shugabannin 'yan bindiga da wasu

Zamfara: Yadda luguden jiragen NAF ya yi ajalin shugabannin 'yan bindiga da wasu

  • Luguden wuta na safiyar Asabar ya lamushe rayukan shugabannin 'yan bindiga Alhaji Auta da Kachalla da suka addabi Birnin Magaji a Zamfara
  • Mazauna yankin sun sanar da cewa, Auta ya na kan babur inda ya ke tare da garken shanunsa yayin da sojoji suka sakar masa bam
  • Mutuwar Auta da Kachalla ta na daya daga cikin manyan nasarorin da sojin saman Najeriya suka samu a cikin kwanakin nan

Birnin Magaji, Zamfara - Luguden wutar jiragen saman sojin sama na Najeriya a sa'o'in farko na ranar Asabar ya yi ajalin rayukan shugabannin 'yan bindiga biyu da wasu miyagun 'yan ta'adda da ke addabar jama'a a karamar hukumar Birnin Magaji ta jihar Zamfara.

Daily Trust a ranar Lahadi ta tattaro cewa, gagararren dan bindiga, Alhaji Auta, ya sheka lahira bayan bam din da jirgin sojoji ya wurga ya tashi da shi yayin da ya ke kan babur tare da shanunsa daga sansaninsu.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Sojoji sun tarwatsa shugabannin 'yan bindiga a Zamfara

Zamfara: Yadda luguden jiragen NAF ya yi ajalin shugabannin 'yan bindiga da wasu
Zamfara: Yadda luguden jiragen NAF ya yi ajalin shugabannin 'yan bindiga da wasu. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Farmakin ya lamushe rayukan wasu 'yan kungiyarsa da ke kusa da sansani da kuma wadanda ke yankin, Daily Trust ta ruwaito.

Samamen da aka kai sansanin Auta ya na daga cikin manyan nasarori da sojin saman Najeriya suna samu, bayan farmakin da ya yi ajalin shugabannin 'yan bindiga Tawaye a Dumburm a makon farko na Disamba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majiyoyi masu tarin yawa sun tabbatar da mutuwar Auta, duk da cewa har yanzu sojoji ba su fitar da takarda kan hakan ba.

Wani mazaunin yankin wanda ya bukaci a boye sunansa, ya sanar da cewa bam din da ya kashe dan bindigan an sako shi ne kansa yayin da ya ke kan titin Nasarawa Mailayi-Gusami.

Sabon farmakin Zamfara: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da mata da diyar lakcara

A wani labari na daban, 'yan bindiga sun tsinkayi yankin Mareri da ke babban birnin jihar Zamfara a ranar Juma'a kuma sun sace mata da diyar wani lakcaran kwalejin ilimi.

Kara karanta wannan

Sabon farmakin Zamfara: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da mata da diyar lakcara

An gano cewa, sun kwashi dukiya daga gidan malamin mai suna Dr Abdulrazak Muazu, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Ba a tabbatar da cewa Muazu ya na gida ko ba ya nan ba lokacin da masu farmakin suka shiga gidansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel