Kano: 'Yan sanda sun kama mutum 362 da ake zargin masu garkuwa ne da 'yan fashi a 2021

Kano: 'Yan sanda sun kama mutum 362 da ake zargin masu garkuwa ne da 'yan fashi a 2021

  • Yan sanda a jihar Kano sun bada kididdigar masu laifi da kame da rundunar ta yi a shekarar 2021 da ta shude
  • Rundunar ta ce ta kama mutum 362 da ake zargi da fashi da makami da garkuwa da mutane a jihar duk dai cikin 2021
  • Yan sandan sun kuma ce sun kama 158 da ake zargi safarar miyagun kwayoyi, 89 masu damfara, 75 masu satar mota, 49 masu satar keke napep, 10 masu satar babur sai 35 masu satar shanu

Jihar Kano - Rundunar yan sandan Najeriya reshen jihar Kano ta ce ta kama mutane 362 da ake zargi da fashi da makami da garkuwa da mutane a shekarar 2021, The Punch ta rahoto.

Mai magana da yawun yan sandan, DSP Abdullahi Haruna, cikin wata sanarea da ya fitar a ranar Lahadi, ya ce cikinsu, 237 ana zargin yan fashi ne yayin da 125 ana zarginsa da garkuwa da mutane.

Kara karanta wannan

‘Yan sanda sun kai samame sansanin ‘yan bindiga a Kaduna, sun ceto mutum 9

Kano: 'Yan sanda sun kama mutum 362 da ake zargin masu garkuwa ne da 'yan fashi a 2021
'Yan sanda a kano sun kama mutum 362 kan laifukan fashi da makami da garkuwa da mutane a 2021. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Wasu da ake zargi da wasu laifukan daban

Haruna ya kuma ce yan sandan sun kama mutane 158 da ake zargin masu safarar miyagun kwayoyi ne, 89 masu damfara, 75 masu satar motocci, 49 masu satar keke napep, 10 masu satar babur sai 35 masu satar shanu.

Ya ce rundunar ta kuma kama wasu mutane 1,576 da ake zargin 'yan daba ne yayin shekarar ta 2021.

Mai magana da yawun yan sandan ya yi bayanin cewa sun ceto mutane 39 da daga hannun masu garkuwa da mutane da safarar mutane.

Ya kara da cewa:

"Rundunar yan sanda ta samu korafi na kisar gilla a gida har 29, inda aka hallaka mutane 31.
"Kazalika, rundunar ta samu korafi na cin zarafi 71, 84 na ayyukan da suka saba wa al'adar dan adam ta kuma kama 'yan Boko Haram biyu."

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi ram da Babuga Yellow, sun bankado yunkurinsu na satar jama'a

Katsina: 'Yan sanda sun kama wani da ke yaudarar mata ya kwana da su a otel ya kuma sace musu waya da kuɗi

A wani labarin, jami'an yan sanda a Jihar Katsina sun kama wani mutum mai shekaru 31 da ake zargin yana amfani da intanet wurin yaudarar mata yana kwanciya da su a Kano, Vanguard ta ruwaito.

An shaida wa manema labarai cewa wanda ake zargin, Usama Tijjani, mazaunin Daurayi Quaters ne a karamar hukumar Gwale a Jihar Kano.

Yan sandan suna zarginsa da:

"Kai 'yan mata otel domin ya kwanta da su sannan ya yaudara su ya sace musu kayayyakin su masu muhimmanci".

Asali: Legit.ng

Online view pixel