'Yan sanda sun yi ram da Babuga Yellow, sun bankado yunkurinsu na satar jama'a

'Yan sanda sun yi ram da Babuga Yellow, sun bankado yunkurinsu na satar jama'a

  • Rundunar 'yan sandan jihar Niger ta yi ram da Babuga Yellow, gagararren dan bindiga da ke cikin kungiyar masu sace mutane a jihar
  • Kamar yadda Umar Mohammed, wanda aka fi sani da Babuga Yellow ya sanar, sun shirya satar wasu fitatun mutane 2 a jihar
  • Yayin tuhumarsa, Yellow ya bayyana sunayen abkan harkallarsa da kuma yadda suke satar shanu a jihar Niger da kewaye

Niger - Rundunar 'yan sandan jihar Niger, ta yi ram da matashi mai shekaru 26 mai suna Umar Mohammed wanda aka fi sani da Babuga Yellow, kan zargin garkuwa da mutane, Punch ta ruwaito.

A wata takarda da kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Wasiu Abiodun, yasa hannu a ranar Juma'a a Minna, wanda ake zargin ya bayyana cewa tawagarsa ta shirya aikata mummunan aiki kafin a kama shi.

Kara karanta wannan

An kama masu garkuwa da mutane yayin da suke jiran kudin fansar wadanda suka sace a Katsina

'Yan sanda sun yi ram da Babuga Yellow, sun bankado yunkurinsu na satar jama'a
'Yan sanda sun yi ram da Babuga Yellow, sun bankado yunkurinsu na satar jama'a. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC
"Ya bayyana cewa, miyagun sun shirya sace wasu fitattun mutane biyu a kauyen Garatu," takardar tace.

Punch ta ruwaito cewa, wanda ake zargin ya kara da bayyana sunayen abokan aikinsa wadanda har yanzu ba a kama su ba, inda ya kara da cewa suna da hannu wurin garkuwa da mutane tare da karbar kudin fansa da kuma satar shanu.

"A yayin tuhuma, ya sanar da cewa ya na cikin kungiyar 'yan bindiga wadanda suka kware da satar shanu tare da satar mutane domin karbar kudin fansa. Ya bayyana sunanyen 'yan kungiyarsu kamar haka: Bokolore, Ruwance, da Giware wadanda yanzu haka basu shigo hannu ba.
"Bayan jerin bincike, ya bayyana cewa sun dinga satar shanu a wurare daban-daban da suka hada da Beji, Wushishi da Kataeregi," Wasiu yace.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Gwarazan yan sanda sun damke kasurgumin dan bindiga da ya addabi Zamfara

Wasiu ya ce 'yan sanda sun yi ram da wani Musa Yakubu mai shekaru ashirin dauke da bindigar toka babu harsasai, inda ya kara da cewa a yayin tuhumarsa da aka yi, ya yi ikirarin cewa ya siya bindigar daga wani wanda bai san sunansa ba amma ya na zama a kauyensu.

Tsagerun yan bindiga sun sake kai harin Tegina, sun yi awon gaba da ma'aikatan ruwa

A wani labari na daban, Dailytrust ta ruwaito cewa aƙalla mutum 5 yan bindiga suka sace a garin Tegina, ƙaramar hukumar Rafi, a jihar Neja.

Idan baku manta ba, a farkon wannan shekaran wasu yan bindiga suka yi awon gaba da ɗaliban makarantar Islamiyya a garin Tegina.

Wata majiya ta bayyana cewa yan bindiga sun sake kai hari garin a ƙarshen makon nan, inda suka sace ma'aikata 5 a wata ma'aikata dake garin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel