Binciken NDDC: Sai an amayo dukkan kuɗaɗen da aka sace, babu sisin kwabo da za mu ƙyalle, Buhari

Binciken NDDC: Sai an amayo dukkan kuɗaɗen da aka sace, babu sisin kwabo da za mu ƙyalle, Buhari

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce za su binciko ko wacce kwabo bayan kammala binciken kididdigar hukumar ci gaban yankin Neja Delta
  • Shugaban kasan ya yi wannan furucin ne a ranar Alhamis a Abuja yayin wani taron kaddamarwar na samfurin dakunan kwana na NDDC a jami’ar Uyo
  • Buhari ya ce za a bincike kasafin daki-daki sannan duk wanda aka kama da sata zai fuskanci fushin hukuma sakamakon yadda wasu suke yasar kudin hukumar yadda su ka ga dama

FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce babu kwabon da zai yi kuka, bayan kammala binciken kudaden Hukumar Bunkasa Yankin Neja Delta, NDDC, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban kasar ya bayyana hakan a Abuja yayin jawabi ta yanar gizo a taron kaddamarwar samfurin dakunan NDDC a jami’ar Uyo da ke Akwa Ibom.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban kasar Gambia zai fuskanci fushin doka saboda kashe wasu 'yan Najeriya

Binciken NDDC: Sai an amayo dukkan kudaden da aka sace, babu sisin kwabo da za mu kyalle, Buhari
Binciken NDDC: Buhari ya ce za a kwato dukkan kudaden da suka yin batan dabo. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Buhari ya ce an kammala kididdigar kuma an gano inda ko wanne kwabo ya sake yayin da ko wanne mai laifi zai fuskanci hukunci daidai da abinda ya aikata.

Akwai wadanda su ka dade su na yashe kudin NDDC tun shekaru 20 da su ka gabata

A cewarsa abin takaici ne yadda aka gano wasu mutane kalilan ne suke ta satar dukiyar hukumar fiye da shekaru 20.

A cewarsa:

“Akwai bukatar hukumar habbaka yankin Neja Delta ta nuna cewa za ta iya yin ayyukanta don kawo gyara a yankin Neja Delta. Da ana amfani da kudaden hukumar da kyau, da yanzu rayuwar mutane da dama ta inganta tunda an kashe biliyoyi a cikin shekaru fiye da 20 da su ka shude.
“Amfani da kudaden yadda bai kamata ba da sata ne ya ke janyo hukumar take kara durkushewa. Don haka za mu fara bincike don gano inda ko wanne kwabo yake bacewa kuma duk wanda muka kama da laifi zai fuskanci fushin hukuma.

Kara karanta wannan

Buhari zai iya kawo karshen ta'addanci kafin cikar wa'adin mulkinsa, Femi Adesina

“Ina son amfani da wannan damar wurin umartar duk wasu ma’aikatan NDDC akan gabatar da duk wata takarda da ta shafi kudi don tabbatar da anyi ga komai kuma an saukaka bincike.”

Wasu kwangilolin an fi shekaru 10 da bayar da su

Buhari ya bayyana hakan ne ta wata takarda wacce kakakinsa, Femi Adesina ya saki inda ya umarci a ci gaba da duk wasu ayyukan da aka dakar sannan a yi duk wadanda ba a fara ba, rahoton Daily Trust.

A cewar shugaban kasar, an bayar da kwangilar ginin dakunan kwanan dalibai maza da mata wadanda za su dauki mutane 1,050 tun shekarar 2004 ne, amma kuma ba a yi ba.

Shugaban kasa ya ce akwai jami’o’i da dama da dalibai su ke fuskantar matsalolin akan rashin dakunan kwana inda suke komawa haya a waje kuma hakan babban nauyi ne ga iyaye ko majibantansu.

Shugaban kasar ya shaida yadda mataimakinsa, farfesa Yemi Osinbajo, a maimakonsa ya kaddamar da aikin Special Protections Unit Base 6 Barrack a Omagwa jihar Ribas, wacce NDDC ta gina kuma ta bai wa hukumar ‘yan sandan Najeriya.

Kara karanta wannan

Kwastam ta yi babban kamu, ta kame kwantena makare da tramadol na biliyoyi

Sanata Akpabio a jawabinsa ya bayyana yadda shugaban kasar ya nuna dagewarsa akan ganin ci gaban rayuwar mutanen yankin Neja Delta.

Buhari: Da zarar na kammala wa'adin mulki na zan koma gona ta a Daura in tare

A wani labarin, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ya na da kudirin komawa gonarsa ta Daura, mahaifarsa da ke jihar Katsina, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban kasa ya furta hakan ne a Istanbul, kasar Turkiyya inda aka shirya masa bikin zagayowar ranar haihuwarsa ba tare da saninsa ba a ofishin jakadancin Najeriya da ke kasar.

Buhari ya na kasar Turkiyya yanzu hakan don halartar wani taro inda har ranar haihuwarsa ta zagayo, ya cika shekaru 79 kenan a ranar Juma’a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel