Buhari zai iya kawo karshen ta'addanci kafin cikar wa'adin mulkinsa, Femi Adesina

Buhari zai iya kawo karshen ta'addanci kafin cikar wa'adin mulkinsa, Femi Adesina

  • Hadimin shugaban kasa, Femi Adesina, ya sanar da cewa mulkin shugaba Buhari zai ga karshen ta'addanci kafin cikar wa'adinsa
  • Adesina ya ce a hankali a ke zakulo 'yan ta'addan kuma lokaci zai zo da za a halaka shugabanninsu, daga nan sai tarihi
  • Hadimin shugaban kasan ya kara da jaddada cewa, shugaban kasa zai inganta rayuwar 'yan Najeriya kamar yadda ya fadi

FCT, Abuja - Femi Adesina, mai magana da yawun shugaban kasa, ya ce yana sa ran za a ga bayan manyan 'yan ta'addan kasar nan kafin cikar wa'adin mulkin shugaban Buhari.

A yayin jawabi a wani shirin Channels TV, Adesina ya ce da irin kokarin da ake yi na inganta tsaro, za a iya ganin bayan rashin tsaro a cikin watanni 17 da suka rage na mulkin Buhari.

Buhari zai iya kawo karshen ta'addancin kafin cikar wa'adin mulkinsa, Femi Adesina
Buhari zai iya kawo karshen ta'addancin kafin cikar wa'adin mulkinsa, Femi Adesina. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC
"Babu abinda ya gagara," yace.
"A lokuta da dama ina gwadawa da Tamil Tigers na Sri Lanka. Wannan 'yan tawayen sun kwashe shekaru 28, amma wata rana kawai aka ga bayan shugabansu, wanda hakan ya kawo karshensu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Wadanda ke da alhakin wannan ta'addancin, za a ga bayansu. Ana zakulo su daya bayan daya kuma za a kai lokacin da za a zakulo dukkansu. Za a iya yin hakan cikin watanni 17 da suka rage wa wannan mulkin."

Adesina ya kara da cewa, shugaban kasa ya na aiki tukuru wurin ganin ya inganta rayuwar 'yan kasa, TheCable ta ruwaito.

"Ina tuna sakon shugaban kasa na Kirsimeti, kun san ya ce ya na kokarin inganta rayuwar 'yan Najeriya," yace.

Buhari: Ba zan huta ba har sai na tabbatar Najeriya ba ta fama da kalubalen tsaro

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa mulkinsa ba zai huta ba har sai kalubalen tsaron da Najeriya ke fuskanta a yanzu ta kawo karshe, Daily Nigerian ta ruwaito.

Buhari, wanda ya samu wakailcin ministan kimiyya da fasaha, Dr Ogbonayan Onu, ya sanar da haka ne a yayin gabatar da wani littafi mai suna "Standing Strong" wanda tsohon shugaban majalisar dattawa, Ken Nnamani ya rubuta a Abuja.

"Muna cigaba da duba hanyoyi da tsarikan cigaba da nakasa dukkan wani karfin 'yan ta'adda a kasar nan," yace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel