Kwastam ta yi babban kamu, ta kame kwantena makare da tramadol na biliyoyi

Kwastam ta yi babban kamu, ta kame kwantena makare da tramadol na biliyoyi

  • Rundunar kwastam ta Najeriya ta yi babban kamu, ta kame wata babbar kwantena makare da miyagun kwayoyi
  • An shirya kwayoyin ne hade da fakitin kunzugun yara da aka shigo dasu daga kasar waje, kamar yadda hukumar ta fada
  • A halin yanzu dai ana ci gaba da bincike domin tantance a hukumar NAFDAC kayan da kuma sanin makama ta gaba

Seme, Legas - Rundunar Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS), sashen Seme, ta ce ta kama wasu kayayyaki da ake zargin kwayoyin tramadol ne da aka boye cikin manyan kunzugun yara a cikin kwantena.

Kayayyakin suna da darajar kudi akalla na Naira biliyan 1.4 da aka lissafa su, Premium Times ta ruwaito.

Kayan da aka kama na Tramadol
Hukumar kwatsam ta yi babban kamu, ta kame kwantena makare da tramadol | Hoto lindaikejisblog.com
Asali: UGC

Jami’in hulda da jama’a na hukumar Kwastam Hussain Abdulahi, a wata sanarwa da ya fitar a Seme, ya ce lambar kwantenar ita ce MRKU 9090415.

Kara karanta wannan

Sabuwar dokar Korona: An hana wuraren ibada da gidajen shakatawa a Abuja taro

Mista Abdullahi ya ruwaito shugaban hukumar Kwastam Bello Jibo yana cewa, a ranar 15 ga watan Nuwamba ne hukumomin jamhuriyar Benin da ke kan hanyar zuwa Najeriya suka mika kwantenar ga hukumar.

Mista Jibo ya ce kwantenar ta zo ne a karkashin kulawar jami’an rundunar saboda babu wani mai shigo da kaya ko wakilinsa da ya zo don aikin tantance kayan.

A cewar sanarwar:

“A ranar 20 ga Disamba, Hukumar Kwastam ta Seme ta gayyaci sauran jami’an tsaro da masu ruwa da tsaki don shaida bincika wata kwantena.
“Abubuwan da aka gano yayin binciken kashi 100 sun hada da fakiti 200 na manya kunzugun yara, katan 100 na Gabadol 120mg wanda ake zargin tramadol ne daidai da 360kg.
“An shirya kunzugun yaran tsaf a gaban kwantenar yayin da magungunan ke baya.

Kara karanta wannan

Bincike ya bayyana asarar biliyoyi da gwamnati ta yi saboda dakatar da Twitter

“Na ba da umarnin a fitar da samfurori a hukumance a mika su ga Hukumar Kula Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) don tantancewa tare da tabbatar da magungunan.”

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito cewa, Kwamandan ya kara da cewa rundunar ta fara gudanar da cikakken bincike da nufin kamo wadanda ke da hannu wajen shigo da su ta haramtacciyar hanya.

'Yan sanda sun yi ram mutum 3 masu safarar miyagun kwayoyi da dillancinsu

A wani labarin, rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta yi ram da wasu matasa uku bisa zarginsu da safarar miyagun kwayoyi cikin jihar Kano ga ‘yan daba.

Rundunar ta bayyana hakan ne ta kakakinta, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce wadanda ake zargin sun hada da Rabiu Idris mai shekaru 22, Abdullahi Muhammad mai shekaru 20 da Sunusi Sani mai shekaru 23 wadanda duk ‘yan asalin jihar Katsina ne daga karamar hukumar Safana.

Kara karanta wannan

Labari da duminsa: Gobara ta yi kaca-kaca da katafaren kamfani a jihar Kano

A cewarsa, cikin miyagun kwayoyin da aka kama su da su sun hada da Tramadol, Exol da Diazepam, inda ya kara da cewa an samu N150,600 daga hannunsu, wanda akwai ‘yan N50, N500 da ‘yan N1000 wadanda duk cinikin kwayoyin ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel