Kungiyar MSSN ta fusata da yadda ake kuntatawa masu hijabi a kudu, za ta dauki mataki

Kungiyar MSSN ta fusata da yadda ake kuntatawa masu hijabi a kudu, za ta dauki mataki

  • Kungiyar dalibai musulmai ta MSSN ta koka kan yadda ake tauye wa musulmi 'yancinsu a makarantun kudu maso yamma
  • Kungiyar ta ce sam ba za ta amince hakan ya ci gaba da faruwa ba, domin kuwa za ta dauki mataki a yanzu kam
  • Kungiyar ta bayyana haka ne ta bakin Amir na kungiyar a wani IVC da aka gudanar a makon nan a yankin kudu maso yamma

Osun - Kungiyar dalibai musulmi ta Najeriya (MSSN) a ranar Lahadi ta sha alwashin yaki da hana sanya hijabi a makarantu a jihohin Kudu maso Yamma, musamman a manyan makarantu.

Amir na MSSN a yankin, Qaasim Odedeji, ne ya bayyana haka a yayin taron Musulunci na IVC karo na 111 mai taken: “How could this be” a sakateriyar MSSN da ke kan titin Legas zuwa Ibadan.

Kara karanta wannan

Allah ya yiwa tsohon Shugaban Majalisar koli ta Shari'a, Dr Datti Ahmad, rasuwa

Kungiyar MSSN ta magantu kan sanya Hijabi a kudu maso yamma
Kungiyar MSSN ta fusata da yadda ake kuntatawa masu hijabi a kudu, za ta dauki mataki | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ya ce wasu masu tauye hakkin addini suna jin dadin amfani da matsayinsu wajen tauye hakkin dalibai musulmi, Daily Trust ta ruwaito.

A nasa jawabin, magatakardar JAMB, Farfesa Isiaq Oloyede, ya koka da yadda ake fama da karancin malaman addinin Musulunci a makarantun gwamnatin Kudu maso Yamma.

Hakazalika, ya kuma koka kan yadda manhajojin makarantun Islamiyyah na gargajiya a wasu sassan suka tsufa da yadda zamani ke tafiya.

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, ya shawarci dalibai da su guji tashin hankali, inda ya bukace su da su kasance masu hange wajen gabatar da jawabai maimakon ta da zaune tsaye.

A nasa jawabin, Gwamna Gboyega Oyetola na Osun ya yaba da gudunmawar da shugabancin kungiyar MSSN ke bayarwa a Najeriya ta hanyar gudanar da ayyukan da'awah a makarantu da ba da ilimi a fadin kasar.

Kara karanta wannan

IGP: Abun tashin hankali ne yadda ISWAP suka iya harba makamai masu linzami a Borno

Madam Noimot Salako, mataimakiyar gwamnan jihar Ogun, ta taya kungiyar MSSN murna kan shirin IVC karo na 111, inda ta bukace su da su jajirce wajen yada kyawawan dabi’u.

CP Olayinka Balogun mai ritaya a laccarsa mai taken ‘Yawaitar rashin tsaro a Najeriya da kuma Tasirin dabi'ar Bil Adama’ ya ce rashin shugabanci nagari na iya haifar da matsalolin rashin tsaro iri-iri.

Gwamnatin Kwara ta umarci malaman makaranta su koma kan aiki

Shugaban hukumar dake kula da malaman sakandire (TSB) na jihar Kwara Bello Abubakar ya umarci daukacin shugabannin makarantu 10 da aka rufe tare da malamansu da su koma bakin aiki ranar 19 ga watan Maris shekarar 2021.

A wani bayani da kakakin hukumar ilmi na jihar, Amogbonjaye Peter, ya fitar, yace ya zama wajibi malaman su koma domin ƙara horar da ɗaliban dake fuskantar jarabawar ƙarshe ta gama sakandire, inji rahoton Punch.

Malam Bello yace duk wani malamin da ya kuskura bai koma ba, to lallai zai fusƙanci fushin hukumar ilmi ta jihar, domin kuwa su ba zasu lamunci rashin ɗa'a ba.

Kara karanta wannan

Kaduna: Hotunan Musulmai da suka halarci coci domin taya Kiristoci murnar Kirsimeti

Sannan ya kirayi jama'a a kan su daina ɗaukar doka a hannun su inda ya kara jaddada cewa lallai ne a cigaba da yin zama tsakanin gwamnati da masu ruwa da tsaki don ganin cewa an samu daidaito.

A wani labarin daban, Gwamnatin jihar Kwara ta baiwa makarantu 10 waɗanda rikicin hijabi ya shafa a kwanakin baya da su koma makaranta yau Litinin 12 ga watan Afrilu.

Gwamnatin ta ce makarantun su koma don cigaba da karatun zango na uku kamar yadda jaridar PM News ta ruwaito.

Sakataren ma'aikatar Ilimi ta jihar, Kemi Adeosun, ta bayyana haka ranar Lahadi, ta ce an ɗauki wannan matakin ne domin ɗalibai su dawo su cigaba da karatunsu kamar yadda yakamata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel