Allah ya yiwa tsohon Shugaban Majalisar koli ta Shari'a, Dr Datti Ahmad, rasuwa

Allah ya yiwa tsohon Shugaban Majalisar koli ta Shari'a, Dr Datti Ahmad, rasuwa

  • Shahrarren Likita kuma dan gwagwarmaya, Dakta Datti Ahmad ya rigamu gidan gaskiya
  • Manyan Maluma a jihar Kano da Najeriya sun yi alhinin mutuwarsa
  • Da dama sun siffantashi mastayin wanda ba za'a taba mantawa da irin gudunmuwar da ya baiwa addinin Musulunci ba

Allah ya yiwa tsohon Shugaban Majalisar koli ta Shari'a a Najeriya (SCSN), Dr Datti Ahmad, rasuwa ranar Alhamis a jihar Kano.

Legit ta tattaro cewa Dr Datti ya rasu ne bayan rashin lafiya da yayi fama.

Diraktan tashar Sunna TV, Dr Abu Aisha Ibrahim Disina a jawabin ta'aziyyarsa ya bayyana cewa za'a yi Sallar jana'iza a Masallacin Al-Furqan dake Kano misalin karfe 10 na safe.

Ya siffanta marigayin a matsayin dan gwagwarmayan kare Musulmai a Najeriya.

Kara karanta wannan

Hotunan mai jinyan da ya sace motar Asibiti a jihar Kano bayan Yan sanda sun damkeshi

A cewarsa:

"Gwagwarmayar kare muradun Musulmai ba za ta manta da kai ba a Nigeria!! Janaza: 10:00am a Masallacin Alfurqan Kano.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Allah ya karbi aiyukanka, Ya kai haske kabarinka, Ya sanya Aljannah ce Makomarka.
Allah ka kiyayemu, mu 'yan baya, Ya sa mu cika da Imani."

Allah ya yiwa tsohon Shugaban Majalisar koli ta Shari'a, Dr Datti Ahmad, rasuwa
Allah ya yiwa tsohon Shugaban Majalisar koli ta Shari'a, Dr Datti Ahmad, rasuwa
Asali: Facebook

Ya taba takarar kujerar shugaban kasa

Marigayin, wanda Likita ne gabanin rasuwarsa ya taba takarar neman kujeran shugabancin kasa.

A 2013, Gwamnatin Jonathan ta nada shi cikin kwamitin da za tayi sulhu da yan Boko Haram amma yace ba zai yi ba saboda gwamnatin ba gaske take ba, a cewarsa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel