IGP: Abun tashin hankali ne yadda ISWAP suka iya harba makamai masu linzami a Borno

IGP: Abun tashin hankali ne yadda ISWAP suka iya harba makamai masu linzami a Borno

  • Sifeta janar na ‘yan sanda, Usman Baba, ya bayyana damuwarsa akan yadda mayakan ISWAP su ka harba makamai masu linzami a wasu yankuna da ke jihar Borno
  • Saura sa’o’i kadan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa jihar Borno mayakan ISWAP suka harba makamai masu linzami a babban birnin jihar Borno
  • Sakamakon hakan, gidaje da dama suka lalace bayan ababen masu fashewa sun tashi a Ngomari, Bulumkutu, Ajilaro da garin Ayafe

FCT, Abuja - Usman Baba, Sifeta janar na ‘yan sanda ya nuna damuwarsa akan yadda mayakan ISWAP su ka harba makamai masu linzami a jihar Borno.

Mayakan ISWAP sun harba makamai masu linzami a garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno ana saura sa’o’i kadan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa Borno, TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Korona ta barke a Aso Rock: Garba Shehu, Lai Mohammed, Dogarin Buhari duk sun kamu

IGP: Abun tashin hankali ne yadda ISWAP suka iya harba makamai masu linzami a Borno
IGP: Abun tashin hankali ne yadda ISWAP suka iya harba makamai masu linzami a Borno. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Gidaje da dama sun lalace sakamakon ababen masu fashewa wadanda suka tayar a wurare kamar Ngomari, Bulumkutu, Ajilari da garin Ayafe, TheCable ta ruwaito.

Yayin amsa tambayoyi akan yadda za a kawo karshe rashin tsaro a fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Baba ya ce tashin rokokin nan abu ne mai ban tsoro.

Sai dai ya ce ‘yan ta’addan ba su samu nasarar cimma burinsu ba.

“Sun dana raukokin a Manyan garuruwa ne da ke Maiduguri. Wannan babbar matsala ce. An yi bincike kwarai a kai kuma ana ci gaba da binciken,” a cewar Baba.
“Eh sun yi iyakar iyawarsu amma ba su samu nasarar abinda su ka so yi ba saboda kokarin jami’an tsaro musamman sojoji.”

Yayin da aka tambaye shi idan jami’an tsaron sun samu nasarar gano inda aka samo raukokin, Baba cewa yayi:

Kara karanta wannan

Buhari ga hafsoshin tsaro: Ku murkushe Boko Haram kafin 2023

“Eh, an taba yin hakan. An fitar da wadanda su ka shirya harba rokokin ko kuma su suka harba su.”

Sifeta janar din ya tabbatar da kokarin da jami’an tsaro su ke yi na ganin sun tabbatar da zaman lafiya da tsaro yayin lokutan shagulgulan karshen shekarar nan.

Ya kara da cewa shugaba Buhari ya bai wa jami’an tsaro umarni akan kada su kuskura su daga wa ‘yan ta’adda kafa.

“Ana rike da wannan umarnin kuma dama haka ake. Babu wata daga kafa tsakanin jami’an tsaro da ‘yan ta’adda.
“Ba za mu sassauta wa ‘yan ta’adda ba don wajibi ne a ci gaba da bibiyarsu don kawo karshen rashin tsaro, garkuwa da mutane da fashi da makamai," a cewarsa.

Boko Haram sun harba makamai masu linzami a filin jirgin Maiduguri

A wani labari na daban, 'yan ta'addan Boko Haram sun harba makamai masu linzami a filin jirgin sama da ke yankin Ngomari a Maiduguri yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke shirin sauka a birnin yau Alhamis.

Kara karanta wannan

‘Yan Boko Haram sun hallaka mutane 5, raunata wasu a ranar da Buhari ya ziyarci Maiduguri

Daily Nigerian ta tattaro cewa, daya da cikin makaman masu linzami ya tsallake har zuwa Ajilari, kusa da filin jiragen sama na Maiduguri inda sansanin sojoji ya ke.

Majiyoyi sun ce mutum daya ya rasa ransa a Ngomari yayin da wasu suka samu raunika a yankin Ajilari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel