Rikicin Hijabi: Madalla! An Buɗe makarantun da rikicin Hijabi ya shafa a Jihar Kwara

Rikicin Hijabi: Madalla! An Buɗe makarantun da rikicin Hijabi ya shafa a Jihar Kwara

- Gwamnatin Kwara ta baiwa makarantu 10 da rikicin hijabi ya shafa a jihar umarni da su koma domin cigaba da karatun zango na uku

- Hakanan kuma gwamnatin ta umarci dukkan malaman dake aiki a waɗannan makarantun da su koma kuma su cigaba da shiga azuzuwansu nan take

- A kwanakin baya dai an samu rikici tsakanin ƙungiyar kiristoci ta jihar da wasu iyayen ɗaliban makarantun kan saka hijabi da ɗalibai musulmi ke yi

Gwamnatin jihar Kwara ta baiwa makarantu 10 waɗanda rikicin hijabi ya shafa a kwanakin baya da su koma makaranta yau Litinin 12 ga watan Afrilu.

Gwamnatin ta ce makarantun su koma don cigaba da karatun zango na uku kamar yadda jaridar PM News ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Kwankwaso ya bar hakkin sama da biliyan 50 na masu kwagilar tituna, Ganduje

Sakataren ma'aikatar Ilimi ta jihar, Kemi Adeosun, ta bayyana haka ranar Lahadi, ta ce an ɗauki wannan matakin ne domin ɗalibai su dawo su cigaba da karatunsu kamar yadda yakamata.

Gwamnatin ta kulle Makarantun guda 10 waɗanda aka samu rikicin na hijabi ne a ranar 10 ga watan Fabrairu saboda dalilin zaman lafiya.

Sai dai gwamnatin bata bayyana ko an warware matsalar saka hijabi a makarantun tsakanin gwamnatin jihar da kuma shugabannin kiristoci, ko ba'a warware ba.

A jawabin sakataren ta bayyana tawagar da zasu tabbatar da buɗe makarantun don ganin komai ya tafi cikin ɗa'a.

Rikicin Hijabi: Madalla! An Buɗe makarantun da rikicin Hijabi ya shafa a Jihar Kwara
Rikicin Hijabi: Madalla! An Buɗe makarantun da rikicin Hijabi ya shafa a Jihar Kwara Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

A jawabin na ta ta ce:

"Muna mai sanar ma iyaye da malaman makarantu 10 da rikicin hijabi ya shafa da cewa za'a koma makarantun ranar 12 ga watan Afrilu domin cigaba da karatun zango na uku 2020/2021."

KARANTA ANAN: Kuɗin Makamai: EFCC ta bayyana dalilin da yasa take Amfani da Otal ɗin da aka ƙwace a hannun Dasuƙi

"Wannan matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na ganin ɗaliban makarantun sun koma don cigaba da karatun da suka rasa ya yin da makarantun su ke kulle."

"Komawa makarantun ya zama wajibi musamman ga ɗaliban dake shirin zana jarabawar fita daga makaranta."

"Ranar komawa makarantun dake jihar waɗanda rikicin bai shafe su ba yana nan kamar yadda gwamnati ta bayyana ranar 26 ga watan Afrilu." inji Adeosun.

Sakataren ta kuma ƙara da cewa dukkan malaman dake koyarwa a makarantun da kuma ma'aikata su koma bakin aiki kuma su cigaba da shiga azuzuwa nan take.

A wani labarin kuma Sarkin Musulmi Ya umarci al'umar Musulmi su nemi jinjirin watan Ramadan ranar Litinin

Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III, ya umarci ɗaukacin al'ummar Musulmi da su fara duba jinjirin watan Ramadana daga ranar Litinin.

Sarkin ya bada wannan umarnin ne ta hanyar shugaban kwamitin bada shawara kan al'amuran addinin musulci na fadarsa dake Sokoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: