'Yan Najeriya sun rage amfani da man fetur a watan Yunin shekarar nan

'Yan Najeriya sun rage amfani da man fetur a watan Yunin shekarar nan

  • Kamfanin man fetur na Najeriya ya bayyana yadda amfani da man fetur a Najeriya ya yi matukar raguwa a watan Yuni
  • Kamfanin yana bayyana alkaluman samar da mai da kuma adadin amfani dashi da aka yi a watan, inda ya ba da rahoto dalla-dalla
  • Kamfanin ya gano haka ne ta hanyar kwatanta amfani da alkaluman amfani da man fetur na watan Mayun shekarar nan

Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC) ya ce an yi amfani da lita miliyan 54.5 na man fetur a watan Yunin 2021 a Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

Wannan yana nufin cewa yawan amfani da man fetur a kullum ya ragu da 17.8m a watan Yuni daga lita 72.3 da ake samu a kowace rana a watan Mayu.

Kara karanta wannan

Bayan shekaru 2 ana wahala, Bill Gates ya fara hango karshen annobar annobar COVID-19

Wata sanarwa da kamfanin na NNPC ya fitar a ranar Lahadi ta ce hakan na daga cikin alkaluman da aka fitar a watan Yunin 2021 na rahoton Kudi da Ayyuka na NNPC na wata-wata (MFOR).

Man fetur a Najeriya
'Yan Najeriya sun rage amfani da man fetur a watan Yunin shekarar nan | Hoto: businessday.ng
Asali: UGC

A cewar rahoton, kamfanin ya ce don tabbatar da ci gaba da samar da wadataccen kayan aikin a fadin kasar, an samar da jimillar lita biliyan 1.63 na mai, wanda ke nufin lita miliyan 54.50 a kowace rana a watan Yunin 2021.

Kamfanin mai na kasa NNPC, a watan Satumba, ya ce ana amfani da lita miliyan 72.3 na man fetur a kullum tare da adadin lita 2.241bn a watan Mayu.

A cikin rahoton na baya-bayan nan na watan Yuni, kamfanin ya kuma sanar da rarar cinikin N141.96bn idan aka kwatanta da gibin N37.46bn a watan Mayu.

Kara karanta wannan

An gurfanar da mutumin da aka kama da ATM 2,863 a Legas

An samu kudaden ne bayan da kamfanin mai na kasa NNPC ya zare kudaden kashewa daga cikin kudaden da ya samu a watan Yuni.

Kudaden shiga na rukunin NNPC ya ragu a watan Yuni da 9.07% ko N89.27bn zuwa N894.64bn idan aka kwatanta da alkaluman watan Mayu.

Kudinta na kashewa ya ragu da kashi 29.32% ko kuma N299.44bn zuwa N721.93bn.

Ta ce an samu karuwar kudaden shiga na hada-hada ne saboda karuwar sayar da danyen mai da Kamfanin Raya Man Fetur na Najeriya (NPDC) ke yi, da kuma karin sayar da iskar gas da Kamfanin Gas na Najeriya (NGC) ya yi.

Haka kuma an samu kyakykyawan aiki daga rukunan Duke Oil da Kamfanin Dillancin Gas na Najeriya (NGMC), dukkaninsu rassan kamfanin NNPC.

A kan batun fasa bututu, an lalata bututun mai guda 47, barnar ta ragu da 26% daga alkaluma 64 da aka samu a watan Mayu 2021.

An fi samun barnar a unguwar Mosimi a Ibadan sai kuma yankin Port Harcourt da kuma yankin Kaduna.

Kara karanta wannan

Najeriya ba ta samu ko sisi ba daga ɗanyen man fetur a watan Satumba, inji NNPC

A sashin iskar gas, an samar da iskar gas kwatankwacin cubic feet biliyan 223.77 (bcf) a watan Yunin 2021 wanda ke nuna matsakaicin abinda ake samu a kullum na daidataccen cubic feet miliyan 7,459.88 a rana.

Gwamnatin Buhari ta sa Facebook ya fara karbar harajin VAT daga 'yan Najeriya masu talla

A wani labarin, bayan sanar da wani sabon kudiri na kudi da ya tilastawa kafafen sada zumunta biyan haraji, Facebook ya sanar da cewa 'yan Najeriua masu tallata hajarsu daga watan Janairu za su kara haraji daga 7.5% bisa 100% a Facebook da kuma Instagram.

Kamfanin na Facebook ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Alhamis, 9 ga Disamba, 2021.

A cewar Facebook, cajin zai shafi wadanda ke siyan yankin talla ne na kasuwancinsu ko na shafukan karan kansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel