Bayan shekaru 2 ana wahala, Bill Gates ya fara hango karshen annobar COVID-19

Bayan shekaru 2 ana wahala, Bill Gates ya fara hango karshen annobar COVID-19

  • Bill Gates ya na ganin COVID-19 ta gama kamarin da za tayi, sai dai abin ya lafa a shekarar 2022
  • Dattijon da ya kafa kamfanin Microsoft ya fitar da wasika, ya na cewa an shiryawa Coronavirus
  • Ba’Amurken ya yaba da yadda aka kirkiro magunguna, amma yace babu adalci wajen yadda ake rabon

United States - Attajiri kuma babban ‘dan kasuwan nan, Bill Gates, yace Duniya ta shirya yadda za ta yaki sababbin nau’ukan cutar COVID-19 irinsu Omicron.

Jaridar Bloomberg tace hakan ya na zuwa ne bayan hukumar lafiya ta Duniya watau WHO, ta nuna damuwar ta a kan hadarin samfurin kwayar Omicron.

A wata wasikar karshen shekara da ya rubuta, Mista Bill Gates yace hakika bullowar Omicron abin damuwa ne, amma yace masana su na aikin bincike a kai.

Kara karanta wannan

Iyayen yara 8 da aka tsinci gawarwakinsu a wata mota sun yi martani kan lamarin

Yace tun da aka fara wannan annoba, ba ayi lokacin da aka yi kyakkyawan tanadi irin yanzu ba.

“Abin da mu ka sani shi ne: A yanzu Duniya ta shirya tsaf domin ta magance samfurori (na cutar COVID-19) masu yiwuwar yin illa.”
“Ina sa ran an zo karshen lamarin. Akwai wauta inda aka yi wani hasashe, amma ina tunanin cutar za ta lafa a cikin 2022.” – Bill Gates.
COVID-19
Bill Gates Hoto: www.voanews.com
Asali: UGC

Gates yace an yi nisa matuka wajen samar da magunguna, ya kuma kara da cewa ba a taba fito da magani aka yada shi a kasashe kamar lokacin annobar nan ba.

Inda matsalar ta ke - Gates

Sai dai Attajirin mai shekara 65 a Duniya ya koka a kan matsalar da ake samu wajen yada magunguna da yadda wasu samfurori suke cigaba da bayyana.

Kara karanta wannan

Yadda mu ka yi da Tinubu a gidansa – Shekarau ya yi magana a game da silar rikicin APC a Kano

Business Insider ta rahoto Bill Gates yana cewa kokarin da aka yi na samar da magunguna (ba daya ba) a shekarar da cutar ta karade Duniya, ikon Ubangiji ne.

A wasikar ta shi, Gates yace abin da ya ci masa tuwo a kwarya shi ne rashin adalci wajen raba magungunan cutar, yace ya kamata a fara alluran ne da tsofaffi.

Omicron ta shigo gari

Idan za a tuna, a ranar 25 ga watan Nuwamba, 2021, hukumar kula da cututtuka masu yaduwa ta kasar Afrika ta kudu (NICD) tace an gano sabon samfurin COVID-19.

Wannan samfuri na B.1.1.529 wanda daga baya aka yi wa lakabi da Omricon, shi ne ‘dan auta a gidan cutar murar mashako ta Coronavirus da ta bayyana a 2019.

Asali: Legit.ng

Online view pixel