An gurfanar da mutumin da aka kama da ATM 2,863 a Legas

An gurfanar da mutumin da aka kama da ATM 2,863 a Legas

  • Hukumar EFCC ta gurfanar da wani Ishaq Abubakar da aka kama da katin ATM 2,683 a filin tashin jirage a cikin Indomie
  • An gurfanar da shi a gaban kotun tarayya da ke Legas ne kan tuhumarsa da aikata laifuka 11 masu alaka da damfarar intanet
  • Abubakar ya musanta dukkan tuhumar da ake masa ya kuma bukaci kotu ta bada shi a hannun beli, alkali ya amince ya daga cigaba da sauraron karar

Legas - Hukumar yaki da rashawa da masu yi wa arzikin kasa ta'annati, EFCC, ta gurfanar da wani Ishaq Abubakar gaban Mai Shari'a P.Lifu na Kotu Trayya da ke zamanta a Ikoyi, kan laifuka 11 da suka shafi intanet.

The Punch ta rahoto cewa jami'an Kwastam ne suka kama wanda ake zargin a ranar 22 ga watan Agustan 2020, a filin tashin jirage na Murtala Mohammed, Legas yana hanyar zuwa Dubai da katin ATM 2.863 da katin waya hudu a cikin kwalin Indomie.

An gurfanar da mutumin da aka kama da ATM 2,863 a Legas
Ishaq Abubakar da aka kama da katin ATM 2,863 a Legas. Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

Mataimakin kwantrola na Kwastam, Abdulmumin Bako ya mika shi ga Hukumar EFCC a ranar 10 ga watan Satumban 2020, Premium Times ta ruwaito.

Bako ya ce:

"Wanda ake zargin, da ya yi ikirarin ya fito daga Kano ne, an gan shi tare da wani da aka hada su domin ya taimaka masa wuce wuraren da ake bincike a filin jirgin.
"Hakan ya ja hankalin jami'an da ke aiki suka dage sai an bincika shi sosai daga bisani aka gano abin da ya boye cikin kwalin na Indomie."

An gano katin ATM 10 cikin 2,863 na sata ne, EFCC

Sanarwar ta kakakin EFCC, Wilson Uwujaren ya fitar ta ce binciken da suka yi ya nuna katin ATM 10 cikin 2,863 na sata ne domin masu shi sun tabbatar cewa katin su ya bata.

An kuma gano cewa wasu mutane ne a Kano suka bashi sauran katin domin ya kai wa abokan huldarsu a Dubai.

Abubakar ya musanta aikata laifin da ake tuhumarsa

Bayan karanto masa tuhumar da ake masa, Abubakar ya ce sam bai aikata laifin ba, hakan yasa mai gabatar da kara, S. Suleiman ya roki kotu ta bada daman a cigaba da tsare wanda ake zargin.

Mai kare shi, George Ochima, ya shaida wa kotu cewa sun shigar da takardar neman bada belinsa.

Kotu ta bada belinsa kan kudi N50m tare da tsayayyu biyu da za a bada belinsa a hannunsu.

Mai Sharia Lifu ya dage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 18 ga watan Fabrairun 2022 inda ya ce a cigaba da tsare wanda ake zargin a gidan yarin Ikoyi har sai ya cika ka'idojin belin.

EFCC na neman wasu 'yan Nigeria 4 ruwa a jallo, ta saki hotunansu

A wani labarin, hukumar yaki da rashawa da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, ta nemi taimakon 'yan Nigeria wurin neman wasu mutane hudu da ta ayyana nemansu ruwa a jallo kan damfara.

Hukumar a shafinta na Facebook, a ranar Litinin, 22 ga watan Nuwamba ta ayyana neman Akpodemaye Ikolo, Donald Olorunkoyede, Owootomo Tomilola Sunday, da Okuafiaka Bright Onyebuchi ruwa a jallo.

EFCC ta ce ana bincikar wadanda ake zargin ne kan laifuka masu alaka da damfara. Hukumar ta bukaci duk wani da ke da bayani mai amfani dangane da inda mutanen suke ya tuntubi ofisoshinta a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel