Gwamnatin Buhari ta sa Facebook ya fara karbar harajin VAT daga 'yan Najeriya masu talla

Gwamnatin Buhari ta sa Facebook ya fara karbar harajin VAT daga 'yan Najeriya masu talla

  • 'Yan Najeriya masu tallata hajarsu a Facebook za su biya karin haraji na 7.5% daga watan Janairun 2022, Facebook ya sanar a wani shafin yanar gizo
  • A cewar Facebook, cajin zai shafi wadanda ke siyan talla ga kasuwancinsu ko kuma na shafukan karan kai
  • Sanarwar ta biyo bayan wani mataki da gwamnatin Najeriya ta dauka na tabbatar da kamfanonin sada zumunta na biyan haraji

Bayan sanar da wani sabon kudiri na kudi da ya tilastawa kafafen sada zumunta biyan haraji, Facebook ya sanar da cewa 'yan Najeriua masu tallata hajarsu daga watan Janairu za su kara haraji daga 7.5% bisa 100% a Facebook da kuma Instagram.

Kamfanin na Facebook ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Alhamis, 9 ga Disamba, 2021.

Mai kamfanin Facebook, Mark Zuckerberg
Wata sabuwa: Masu tallata abubuwansu a Facebook za su fara biyan harajin kashi 7.5 | Hoto: nairametrics.com
Asali: Facebook

A cewar Facebook, cajin zai shafi wadanda ke siyan yankin talla ne na kasuwancinsu ko na shafukan karan kansu.

Kara karanta wannan

Babbar magana: 'Yan sanda sun shiga damuwa bayan jin shuru na albashin Nuwamba

Wani bangare na sanarwar yana cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Saboda aiwatar da sabon tsarin haraji (VAT) a Najeriya, ana bukatar Facebook ya biya harajin VAT kan tallace-tallacen ga masu tallata hajarsu, ba tare da la'akari da sayen talla don kasuwanci ko na karan kai ba."
"Daga ranar 1 ga watan Janairun 2022, duk masu tallata hajarsu da ke gudanar da harkokin kasuwanci a Najeriya za a rika biyankashi 7.5 na VAT."

Facebook hakazalika a cikin sakon ya kara da cewa mutanen da harajin VAT ba ya kansu za a iya dawo musu da kudadensu idan sun ba da shaida harajin, inji rahoton TheCable.

"Idan kana da rajistar VAT kuma ka ba da ID na VAT, ID din VAT dinka zai bayyana akan shaidar biyan tallan ku."
"Idan har kuna da damar dawo da VAT din, wannan na iya taimaka muku ku dawo da duk wani VAT da kuka biya wa hukumomin haraji na Najeriya idan kuna kasuwanci ne mai rijistar VAT a Najeriya."

Kara karanta wannan

Rahoton ‘yan sanda: Dalibai biyu sun mutu, 12 sun jikkata a hatsarin babbar mota ranar Talata

CBN ya ba bankin Sterling damar aiki a matsayin bankin Muslunci a Najeriya

A wani labarin, Babban bankin Najeriya (CBN) ya bukaci bankin Sterling Plc da ya ci gaba da aiwatar da shirinsa na gyarawa tare da gudanar da lasisinsa domin kirkirar tsarin mu'amala ba kudin ruwa.

Amincewar bisa ka'ida ce kuma karkashin amincewar tsarin CBN.

Sabon reshen na bankin Sterling da za a kira shi da Alternative Bank Limited zai kuma yi aiki a karkashin ka'idodin addinin Musulunci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel