Babu kasar da ta sayi ɗanyen mai daga Najeriya a watan Satumba, NNPC

Babu kasar da ta sayi ɗanyen mai daga Najeriya a watan Satumba, NNPC

  • Kamfanin NNPC na ƙasa ya fitar da alƙaluman kasuwanci, siye da siyarwa, na watan Satumba
  • A rahoton da kamfanin ya saka a shafin yanar gizo, NNPC ya bayyana cewa duk da hako ɗanyen mai sama da ganga miliyan daya a rana, babu wanda ya siya
  • Alkaluman da NNPC ya bayyana ya hasko rahoton ofishin Akanta Janar a 2019, wanda ya kalubalanci cewa meyasa babu kudin gangan miliyan 104.48

Abuja - Najeriya ba ta samu ko sisi a matsayin kudin shiga ba daga ɗanyen man fetur ɗin da take fitarwa a watan Oktoba duk da ana haƙo aƙalla ganga miliyan N1.417 a kowace rana a watan Satumba.

Kamfanin NNPC ne ya bayyana haka a cikin rahoton da ya gabatarwa kwamitin asusun tara kuɗaɗen shiga na gwamnatin tarayya (FAAC).

Hakan ya yi kama da abinda ya faru a 2019, inda NNPC ya gaza bada ba'asin gangar ɗanyen mai miliyan biyu da aka fitar, kamar yadda yake a rahoton baya-bayan nan da ofishin Akanta Janar (AGF) ya fitar.

Kara karanta wannan

Matashin Fasto ya yi garkuwa da babban Bishop na Katolika a jihar Imo

Kamfanin NNPC
Babu kasar da ta sayi ɗanyen mai daga Najeriya a watan Satumba, NNPC Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Shekaru da dama da suka shuɗe, kasashen Indiya, China, da kuma kasar Amurka, sune suka kasance masu siyan ɗanyen mai da Najeriya ke samarwa.

Wani sashin rahoton NNPC yace:

"Cinikin siyarwa: Bamu samu kudin shiga daga ɗanyen man da Najeriya ta haƙo ba a watan Satumba, 2021."

Rahoton ya bayyana cewa adadin man da Najeriya ta fitar a watan Satumba, 11.49Mbbls, ya nuna an samu ƙarin kashi 98% idan aka kwatanta da 5.79Mbbls da aka hako a watan Agusta.

Sauran hanyoyin samun kudin shiga a NNPC

Duk da kuɗaɗen da NNPC ke samu ta hanyar siyar da mai ga kasashen duniya, rahoton yace kimanin biliyan N252.96bn ne harajin ɗanyen mai da Gas a watan Oktoba.

NNPC yace:

"Gas: A bangaren gas da sauran su, mun samu jumulla biliyan N6.78bn. A watan mun samu N4.07bn daga Gas.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ƴan ta'addan ISWAP sun sace ma'aikatan gwamnatin Jihar Borno

"NLNG: Mun siyar da albarkatun mai da suka kai kimanin dala miliyan $59.43m ga NLNG a tsawon wannan lokacin, inda a ciki mun karbi dala miliyan $52.57. Ragowar an biya kuɗin MCA da sauransu."
"Sauran sune: Kimanin dala miliyan $95.63m na abubuwa daban-daban, Gas da ƙidin ruwa, sun shigo asusu a watan Oktoba."

Abinda muka ƙashe - NNPC

A bangaren kuɗaɗen da kamfanin ya kashe kuma NNPC ya bayyana cewa gyaran bututun mai ya tashi zuwa biliyan N7.75bn.

"Bututu daban-daban sun lakume miliyan N143.38 ƙuma kuɗin sun yi ƙasa da biliyan N163.7bn da akai tsammani."
"Baki ɗaya adadin da suka lakume ya kama biliyan N123.7bn a watan Satumba, kuma biliyan N40bn da suka rage an cike na watan Yuli."

A wani labarin kuma Tsohon Minista a Najeriya, Bunu Sherrif Musa, ya rigamu gidan gaskiya yana da shekara 74 a duniya.

Tsohon ministan ya jagoranci ma'aikatun gwamnatin tarayya da suka haɗa da ma'aikatar Lantarki, hakar ma'adanai da cigaban ƙarafa.

Kara karanta wannan

Yawan 'yan Najeriya na bamu tsoro, dole mu yi wani abu, inji gwamnatin Buhari

Sakataren kungiyar dattawan jihar Borno, Dakta Bulama, yace wannan rasuwa ta zo musu bagatatan, mutum 2 kenan cikin kankanin lokaci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel