Fuskokin wasu kasurguman masu garkuwa da mutane da aka yi ram dasu a jihar Ribas

Fuskokin wasu kasurguman masu garkuwa da mutane da aka yi ram dasu a jihar Ribas

  • Jami'an IRT da na 'yan sanda a jihar Ribas sun yi nasarar kama wasu mutane hudu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne
  • Wadanda ake zargin kan yi amfani da shafukan Facebook da WhatsApp wajen yaudarar mutane musamman mata sannan su yi garkuwa da su don karbar kudin fansa
  • A cikin haka, har sukan yi wa wasun su fyade da kuma dukan tsiya

Ribas - Jami’an rundunar IRT tare da hadin gwiwar jami’an yan sandan jihar Ribas sun kama wasu kasurguman masu garkuwa da mutane da suka shahara wajen amfani da Facebook da WhatsApp don yaudarar mutane a Port Harcourt.

A yayin amsa tambayoyi, wadanda ake zargin sun yarda cewa sun yi garkuwa, lallasawa, fyade da kuma yi wa wadanda suka shiga hannunsu fashi.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane 5 a daji bayan an kai musu tsegumi

Fuskokin wasu kasurguman masu garkuwa da mutane da aka yi ram dasu a jihar Ribas
Fuskokin wasu kasurguman masu garkuwa da mutane da aka yi ram dasu a jihar Ribas Hoto: PM News
Asali: Facebook

Sun yarda cewa sun fi aiwatar da nufinsu kan mata kuma sun yi nasarar karbar kudin fansa daga akalla mata 10 tun daga Janairun 2021. Sannan kudin fansa mafi tsoka da suka karba shine naira miliyan 5, rahoton PM News.

Sunayen masu laifin da aka kama sune: Izunna Fidelis mai shekaru 21, Humble Unity Okeregwu mai shekaru 24, Izuchukwu Nwaobiri mai shekaru 22 da Chibeze Nwike mai shekaru 23.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda suke yaudarar mutane har su fada tarkonsu

An kama su a yankunan Choba da Etche da ke jihar Ribas.

A cewar ‘yan sanda, masu laifin kan ja hankalin mutane a shafukansu na Facebook inda suke badda kamanni a matsayin yan kasar waje da ke aiki da kamfanonin man fetur a jihar Ribas.

Daga nan sai suce suna son yan matan da suka hadu da su tare da neman auren yan matan nasu na Facebook, duk a kokarinsu na dana masu tarko.

Kara karanta wannan

An kama miji da mata da suka hada kai don siyar da ‘ya’yansu mata kan N700,000

‘Yan sandan sun ce an kama su ne bayan rahoton garkuwa tare da yiwa wata mai shekaru 27 mai suna Happiness fyade a ranar 28 ya watan Agusta, 2021.

A cewar jagoran yan ta’addan, Nwaobiri:

“Abun da muke fara yi shine duba hotunan kyawawan mata a Facebook. Daga nan sai mu fara binsu a jerin abokanmu. Kowannenmu na aiki a matsayin mutum daban. Zan fara hira da budurwa, bayan mun gaisa sai na fada mata cewa ina aiki da kamfanin man fetur. Sai na kuma tambayeta tana da aure ko bata da shi.
“Yana daukar lokaci kafin sabawa da su, watanni biyu zuwa uku. Daga nan, sai mu koma hira ta WhatsApp sannan kira ta lambar waya bayan mun gina abota, Za mu gayyace su zuwa kamfanin wanda yake daji inda za a kama su sannan a kira yan uwansu.
“Na fara a farkon shekarar nan saboda yanayi. Mahaifiyata ta mutu, mahaifina na fama da shanyewar barin jiki kuma nine ke daukar dawainiyar komai. Na kasance da hannu a lamura bakwai amma na cimma nasara a hudu.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Masu garkuwa sun kashe tsohon mai neman takarar gwamnan Zamfara a hanyar Abuja zuwa Kaduna

“Muna yiwa wadanda muka kama fyade ne kawai idan suka ki bayar da hadin kai. Wato, idan suka ki matsawa yan uwansu don su biya kudin fansa."

'Yan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane 5 a daji bayan an kai musu tsegumi

A wani labarin, jami'an rundunar yan sandan jihar Ogun sun kama mutum biyar cikin wasu gungun masu garkuwa da mutane da ke adabar Obadda Oko da kewaye a karamar hukumar Ewekoro na jihar, Daily Trust ta ruwaito.

An kama wadanda ake zargin - Aliu Manya, Usman Abubakar, Abayomi Olayiwola, Nasiru Muhammad da Bello Usman bayan yan sandan hedkwata da ke Obada Oko sun samu bayanai.

Daily Trust ta rahoto cewa an tsegunta wa yan sandan cewa an hangi wasu mutane kan babura biyu a cikin daji da ke Eleja kusa da Obada Oko misalin karfe 8 na daren ranar Talata.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifin tsohon mataimakin gwamnan jihar Imo

Asali: Legit.ng

Online view pixel