An kama miji da mata da suka hada kai don siyar da ‘ya’yansu mata kan N700,000

An kama miji da mata da suka hada kai don siyar da ‘ya’yansu mata kan N700,000

  • Jami'an hukumar NSCDC, reshen jihar Akwa Ibom sun kama wani mutum mai suna Elisha Effiong bisa zargin hada kai da matarsa don siyar da yaransu biyu
  • Sai dai sun ce talauci da wahalar rayuwa ne suka kai su ga yanke wannan shawara
  • Jami'an tsaro sun yi nasarar kama su ne bayan sun samu wani bayanan sirri kan shirin nasu

Jihar Akwa Ibom - Jami'an sashin da ke yaki da fataucin mutane na hukumar NSCDC, reshen jihar Akwa Ibom sun kama wani mutum mai suna Elisha Effiong.

Jami'an tsaron sun damke magidancin ne bisa zargin hada kai da matarsa wajen siyar da yaransu mata biyu yan shekaru 6 da 4.

An kama miji da mata da suka hada kai don siyar da ‘ya’yansu mata kan N700,000
An kama miji da mata da suka hada kai don siyar da ‘ya’yansu mata kan N700,000 Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Punch ta rahoto cewa an kama Effiong, wanda ke zaune a Kamaru tare da matarsa a Uyo, babbar birnin jihar a ranar 15 ga watan Nuwamba, bayan samun wani bayanan sirri yayin da yake kokarin siyar da yaransu masu suna Abasifreke Edet da Rachael Edet.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Masu garkuwa sun kashe tsohon mai neman takarar gwamnan Zamfara a hanyar Abuja zuwa Kaduna

A cikin wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na rundunar, Umana Ukeme, ya saki a ranar Laraba, wadanda ake zargin sun bayyana cewa sun yanke shawarar siyar da yaran nasu ne saboda tsananin wuyan da suke ciki.

A cewar sanarwar, wanda ake zargin ya sanar da wani jami'in tsaro mai zaman kansa shirinsa yayinda shi kuma ya sanar da kwamandan rundunar, Mista Abidemi Majekodunmi wanda yayi umurnin kama mai laifin.

Sanarwar ta ce:

"An kama wanda ake zargin, Elisha Edet Effiong, tare da yaransa biyu masu suna Abasifreke Edet, 6, da Rachel Edet, 4 yayin da yake kokarin siyar da su kan N700,000 a Uyo, jihar Akwa Ibom.
"An kama Effiong mai shekaru 40 a asibitin FulCare hanyar unguwar Ekpanya, inda ya sanar da wani mai tsaro kudirinsa na siyar da yaransu biyu domin ya biya bashi da kuma magance matsalolin rashin kudi.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifin tsohon mataimakin gwamnan jihar Imo

"Mai tsaron ya sanar da NSCDC sannan kwamanda Abidemi Majekodunmi ya sanar da jami'an sashin yaki da fataucin mutane na rundunar wadanda suka shiga aiki nan take sannan suka kama wanda ake zargin tare da yaran nasa su biyu."

A cewar Ukeme, an gudanar da binciken farko yayin da za a mika lamarin zuwa ga ofishin NAPTIP reshen Uyo domin hukunta mai laifin, PM News ta rahoto.

Kwamandan yayin da yake yabawa mai tsaron mai zaman kansa kan sanar da su kan lokacin ya kuma yi Allah-wadai da lamarin inda ya bayyana shi a matsayin cin zarafin dan adam.

Ya yi kira ga mutanen jihar Akwa Ibom da su dunga taimakawa jami'an hukumar da bayanan sirri da zai taimaka wajen kama masu laifi a jihar.

Bidiyon yadda dattijuwa ta shiga hannu yayin da aka cafke ta da jaririn sata

A wani labarin, fusatattun matasa sun far ma wata dattijuwar mata bayan an kama ta dauke da jariri sabon haihuwa da ta sato.

Kara karanta wannan

Rikicin APC: 'Yan sanda sun mamaye sakateriyar jam'iyyar APC a Abuja

Labarin wanda shafin lindaikejiblogofficial ya rahoto ya nuna cewa da kyar aka kwaci matar mai suna Roseline daga hannun matasan bayan kama ta da suka yi da jinjirin a yankin Upper Iweka, Onitsha, jihar Anambra.

Asali: Legit.ng

Online view pixel