'Yan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane 5 a daji bayan an kai musu tsegumi

'Yan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane 5 a daji bayan an kai musu tsegumi

  • Yan sanda sun yi nasarar kama wasu mutane biyar da ake zargin masu garkuwa da mutane ne
  • Yan sandan sun kama su ne bayan mutanen gari sun kai rahoton cewa sun hangi mutane da babura cikin daji da dadare
  • Bayan an kamo su, wasu daga cikin mutanen gari sun gane fuskokin wasu daga cikinsu a matsayin wadanda suka taba sace 'yan uwansu

Ogun - Jami'an rundunar yan sandan jihar Ogun sun kama mutum biyar cikin wasu gungun masu garkuwa da mutane da ke adabar Obadda Oko da kewaye a karamar hukumar Ewekoro na jihar, Daily Trust ta ruwaito.

An kama wadanda ake zargin - Aliu Manya, Usman Abubakar, Abayomi Olayiwola, Nasiru Muhammad da Bello Usman bayan yan sandan hedkwata da ke Obada Oko sun samu bayanai.

'Yan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane 5 bayan an kai musu tsegumi
Wasu masu satar mutane 5 sun fada komar 'ya sanda a Ogun. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Daily Trust ta rahoto cewa an tsegunta wa yan sandan cewa an hangi wasu mutane kan babura biyu a cikin daji da ke Eleja kusa da Obada Oko misalin karfe 8 na daren ranar Talata.

Kakakin yan sandan, Abimbola Oyeyemi, a ranar Laraba a Abeokuta ya ce bayan samun bayanan, DPO na Obada Oko, CSP Tijanni Muhammed ya tura jami'ansa tare da mafarauta, yan sa-kai zuwa dajin inda suka kamo mutum biyar da ake zargin.

Abin da aka kwato hannun masu garkuwan

Ya ce an kwato tramadol, ganye da ake zargin wiwi ne, adduna uku, babura biyu masu lamba 504 VC da ODE 423 VC da kudi naira dubu saba'in da uku daga hannunsu.

Wasu da aka taba yin garkuwa da su a baya sun gane su

Hakzalika, ya ce yayin da ake bincike wani da aka taba garkuwa da shi a baya aka sako shi ya zo ya nuna wdanda suka sace shi a cikinsu.

"Dan uwansa, wanda shine ya kai musu kudin fansar shima ya gano mutum biyu daga cikinsu ya ce sune suka karba kudi daga hannunsa kafin aka sako dan uwansa," a cewar sa.

Oyeyemi ya kuma ce kwamishinan yan sanda Lanre Bankole ya bada umurnin a mayar da su sashin binciken masu garkuwa da manyan laifuka.

Kwamishinan ya kuma bada umurnin a cigaba da farautar sauran mambobin tawagar masu garkuwar.

Basarake a Arewa ya haramta bukukuwa cikin dare a ƙasarsa saboda harkokin ƙungiyoyin asiri

A wani rahoton, Mai garin Lokoja, Alhaji Mohammed Kabiru Maikarfi III, ya dakatar da yin duk wani sha’ani da dare a cikin garin Lokoja da duk wasu anguwanni da su ke da makwabtaka da Lokoja har sai yadda hali ya yi.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, ya bayar da umarnin nan ne sakamakon yadda ya ga bata gari su na amfani da damar shagulgulan dare wurin cutar da jama’a a cikin babban birnin jihar.

Kungiyoyin asiri su kan yi amfani da damar bukukuwan dare da sauran sha’anoni a Lokoja da kewaye wurin kai wa jama’a farmaki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel