Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya yabi Jonathan, ya ce kamarsa daban ne a kasar nan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya yabi Jonathan, ya ce kamarsa daban ne a kasar nan

  • Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya taya tsohon shugaban kasar Najeriya murnar cika shekaru 64 a duniya
  • Ya bayyana cewa, tsohon shugaban na daban ne, kuma samun irinsa ba karamin al'amari bane a cikin mutane
  • Ya bayyana yadda Goodluck Jonahan ya bambanta da sauran mutane wajen mayar da hankali kan shugabanci

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan murnar cika shekaru 64 da haihuwa wanda ke zuwa a ranar 17 ga Nuwamba, 2021.

Shugaban, a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata ta hannun mai magana da yawunsa, Femi Adesina, ya taya shi murnar yi wa kasa hidima, da kuma kokarin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban dimokuradiyya a nahiyar Afirka.

Read also

Yajin aikin ASUU: Kakakin majalisa ya gayyaci ministar kudi, na ilimi da shugaban ASUU

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya yabi Jonathan, ya ce kamarsa daban ne a kasar nan
Shugaban kasa Muhammadu Buhari | Hoto: premiumtimesng.com
Source: UGC

A cewar wani yankin sanarwar:

"A madadin gwamnati da 'yan Najeriya, shugaban kasa Muhammadu Buhari yana mika gaisawa da tsohon shugaban kasa, Dr Goodluck Ebele Jonathan da murnar cika shekaru 64 da haihuwa, 17 ga watan Nuwamba, 2021."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Buhari ya ce Jonathan ya ci gaba da fadada iyakokin shugabanci ta hanyar koya wa da dama daga cikin kasar karfin mayar da hankali, daidaito da kuma himma.

Ya yaba yadda Jonathan ya zama mataimakin Gwamna, Gwamna, Mataimakin Shugaban kasa, Shugaban kasa, Wakilin Tarayyar Afirka, kuma yanzu ya zama Shugaban taron kasa da kasa Majalisar Amincin Afirka (ISCP-Africa).

ISCP-Africa kungiya ce ta masu rike da madafun iko da tsoffin shugabannin kasa da mataimakansu, wacce kungiyar zaman lafiya ta duniya ta kafa a shekarar 2019, a matsayin babbar kungiyar tuntuba tare da Majalisar Dinkin Duniya (UN).

Read also

Gwamnan Kogi ya yi wa 'yan siyasa fallasa, ya bayyana alakarsu da rashin tsaron Najeriya

Shugaban ya ce tsarin tsohon shugaban kasar ya kamata ya zama abi koyi ga masu rike da mukamai da duk wasu shugabanni masu kishin kasa cewa yi wa kasa hidima da mutuntaka na bukatar sadaukarwa, da fifita bukatun wasu sama da bukatun kashin kai.

Buhari wanda ya kuma aike da gaisuwar gaisuwa zuwa gare shi da iyalansa, ya yi addu’ar Allah ya kara musu lafiya da koshin lafiya.

Rasuwar kanin Dangote: Buhari ya mika sakon jaje da jimami ga dangin Dangote

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon ta'aziyya ga iyalai da dangin Alhaji Aliko Dangote kan rashin da suka yi a makon nan.

A jiya Lahadi 14 ga watan Nuwamba ne rahotanni suka bayyana cewa, wani daga cikin kannen Alhaji Aliko Dangote ya rigamu gidan gaskiya.

Marigayi Sani Dangote, ya kasance mataimakin shugaba a rukunin Dangote.

Source: Legit.ng

Online view pixel