Gwamnan Kogi ya yi wa 'yan siyasa fallasa, ya bayyana alakarsu da rashin tsaron Najeriya

Gwamnan Kogi ya yi wa 'yan siyasa fallasa, ya bayyana alakarsu da rashin tsaron Najeriya

  • Gwamnan Kogi, Yahaya Bello, ya ce kashi casa'in na matsalar tsaron Najeriya duk 'yan siyasa ne suka kirkiro su kuma sai da siyasa za a magance
  • A cewarsa, babu shakka Boko Haram, 'yan bindiga, kashe-kashe, rikicin manoma da makiyaya suna bukatar siyasa wurin magance su
  • Ya bukaci a jinjina wa shugaban kasa Buhari kan yadda ya tarar da matsalar tsaro da ta tattalin arziki amma ya dage domin magancesu

Kogi - Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello ya ce sama da kashi casa'in na matsalolin tsaron da kasar nan ke fuskanta suna da alaka da siyasa kuma sai da siyasa za a iya shawo kan lamarin.

Gwamnan ya jinjina wa shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya gaji siyasa a hargitse da kuma tattalin arziki mara kyau amma ya ke kokarin ganin ya gyara.

Read also

Na jinjinawa bajintarsu: Buhari ya yi makokin sojojin da mayakan ISWAP suka kashe

Kamar yadda Tribune ta ruwaito, Gwamna Bello ya sanar da hakan ne yayin da ya karba bakuncin kungiyar mafarautan Najeriya wadanda suka bashi kambun girmamawa kan kokarinsa na tsare jihar Kogi.

Gwamnan Kogi ya yi wa 'yan siyasa fallasa, ya bayyana alakarsu da rashin tsaron Najeriya
Gwamnan Kogi ya yi wa 'yan siyasa fallasa, ya bayyana alakarsu da rashin tsaron Najeriya. Hoto daga tribuneonlineng.com
Source: UGC
"Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karba mulkin kasar nan yayin da ake fama da matsalar tsaro, tattalin arziki da sauransu. Shugaban kasa ya gaji kasar da ake dasa bama-bamai a kowacce rana a yankin arewa maso gabas har da Abuja.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Shugaban kasa ya gaji tsarin tsaron da ya rube, babu kayan aiki kuma babu horarwa. Shugaban kasa ya duba dukkan wani bangaren walwala na hukumomin tsaron kasar nan.
“Cike da tabbaci zan iya cewa kashi casa'in na rashin tsaron da ake fuskanta a kasar nan yana da alaka da siyasa. Daga kan Boko Haram, 'yan bindiga, rikicin makiyaya da manoma da kashe mutane har da garkuwa da mutane," Gwamnan yace.

Read also

Kungiyar PDP ta nemi Gwamna Wike ya nemi takarar kujerar shugaba Buhari a 2023

Ya ce a matsayinsa na gwamna, ya fuskanci rashin tsaro masu alaka da siyasa amma ya iya shawo kan matsalar rashin tsaro, Tribune ta wallafa.

"Ya kamata mu jinjinawa shugaban kasa kan kalubalen da ya ke fuskanta. Ni ma na fuskanci irin wadannan kalubalen lokacin da na hau kujera ta. Banbancin shi ne ina da burin ganin bayansu kuma kai tsaye na magance su.
“Idan muka kula da rashin tsaro na siyasa, sauran kashi goman zai kula da kanshi," Gwamna Bello yace.

Buhari: Ba zan huta ba har sai na tabbatar Najeriya ba ta fama da kalubalen tsaro

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa mulkinsa ba zai huta ba har sai kalubalen tsaron da Najeriya ke fuskanta a yanzu ta kawo karshe, Daily Nigerian ta ruwaito.

Buhari, wanda ya samu wakailcin ministan kimiyya da fasaha, Dr Ogbonayan Onu, ya sanar da haka ne a yayin gabatar da wani littafi mai suna "Standing Strong" wanda tsohon shugaban majalisar dattawa, Ken Nnamani ya rubuta a Abuja.

Read also

Kungiyar mata 'yan jarida sun koka kan tsadar rayuwa, sun mika bukatarsu ga gwamnati

"Muna cigaba da duba hanyoyi da tsarikan cigaba da nakasa dukkan wani karfin 'yan ta'adda a kasar nan," yace.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel