Yajin aikin ASUU: Kakakin majalisa ya gayyaci ministar kudi, na ilimi da shugaban ASUU

Yajin aikin ASUU: Kakakin majalisa ya gayyaci ministar kudi, na ilimi da shugaban ASUU

  • Kakakin majalisar wakilan Najeriya ya bayyana bukatar ganawa da wasu manyan jami'an gwamnati uku
  • Zai gana da ministan ilimi da ministar kudi kana da shugaban kungiyar malaman jami'o'in Najeriya wato ASUU
  • Zai gana dasu ne kan batun yajin aikin da ASUU tace za ta tsunduma saboda gazawar gwamnati wajen biya mata bukata

Abuja - Jaridar Punch ta ruwaito cewa, kakakin majalisar wakilai, Hon. Femi Gbajabiamila ya gayyaci ministar kudi, kasafi da tsare-tsare ta kasa, Mrs Zainab Ahmed da Ministan Ilimi, Adamu Adamu domin zaman gaggawa.

Hakazalika, ya gayyaci Shugaban Kungiyar Malaman Jami’o’i, Farfesa Emmanuel Osedeke, a wani taron gaggawa a ranar Alhamis, 18 ga Nuwamba, 2021.

Da Duminsa: Kakakain majalisa ya gayyaci ministar kudi, na ilimi da shugaban ASUU
Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila | Hoto: dailypost.ng
Asali: Twitter

An gayyaci shugaban ASUU ne kan barazanar yajin aikin da malaman jami’o’in suka yi a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Jami'ar Ilorin ta kori dalibin dan aji hudu da ya lakadawa lakcararsa dukan kawo wuka

Gbajabiamila ya bayyana hakan ne a zauren taron a ranar Talata bisa kudirin gaggawa na muhimmancin jama’a da shugaban kwamitin majalisar kan harkokin ilimi Farfesa Julius Ihonvbere ya gabatar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ihonvbere ya roki majalisar da cewa ta bukaci:

“Gwamnatin tarayya da ta gaggauta daukar duk matakan da suka dace don bude tattaunawa ta gaskiya da ASUU don dakatar da yajin aikiN da kuma aiwatar da yarjejeniyar da aka yi domin amfanin dalibanmu da iyayensu da bangaren ilimi da kuma kasa baki daya.”

A hukuncin da ya yanke bayan ‘yan majalisar sun amince da kudurin baki daya, shugaban majalisar ya ce:

“Ya kamata kwamitocin ilimi, manyan makarantu da kanana, su yi bincike su kai rahoto ga majalisa. Zan gana da Ministan Kudi da Ministan Ilimi da kuma wakilan kungiyar ASUU a ofishina ranar Alhamis.”

Majalisar ta ce zata yi duk mai yiyuwa wajen ganin ta dakile afkuwar yajin aikin da ASUU ta yi ikrarin tsundumawa.

Kara karanta wannan

EndSARS: Jerin sunayen wadanda Soji suka kashe a Lekki Toll Gate, Kwamitin Bincike

Idan baku manta ba, mun kawo muku rahoton cewa, kungiyar malaman jami’o’in Najeriya ASUU ta baiwa gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki 21 kan gazawar gwamnati wajen aiwatar da yarjejeniyar da suka yi, kamar yadda Channels Tv ta ruwaito.

ASUU: Malaman Jami’a za su hadu da Gwamnati a kan yiwuwar sake shiga yajin-aiki

A watan Satumba, bayan tsawon makonni babu wata magana tsakanin gwamnatin tarayya da malaman jami’o’i, kungiyar ASUU tace za suyi wani zama a makon nan.

Bangarorin za su tattauna kan rashin cika alkawuran da gwamnatin tarayya ta dauka a lokacin da aka janye wani dogon yajin-aiki a Disamban shekarar 2020.

Shugaban kungiyar ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke ya kyankyasawa manema labarai wannan a lokacin da ya yi magana da jaridar Nigerian Tribune.

Asali: Legit.ng

Online view pixel