Rasuwar kanin Dangote: Buhari ya mika sakon jaje da jimami ga dangin Dangote

Rasuwar kanin Dangote: Buhari ya mika sakon jaje da jimami ga dangin Dangote

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon ta'aziyya ga iyalai da 'yan uwan Alhaji Aliko Dangote
  • A jiya ne aka samu labarin mutuwar kanin Aliko Dangote, Sani Dangote Wanda shi ma shugaba ne a rukunin Dangote
  • Shugaba Buhari ya jajanta, tare da ba iyalan marigayin hakuri da kuma yi masa addu'ar Allah ya jikansa da rahama

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon ta'aziyya ga iyalai da dangin Alhaji Aliko Dangote kan rashin da suka yi a makon nan.

A jiya Lahadi 14 ga watan Nuwamba ne rahotanni suka bayyana cewa, wani daga cikin kannen Alhaji Aliko Dangote ya rigamu gidan gaskiya.

Rasuwar kanin Dangote: Buhari ya mika sakon jaje da jimami ga dangin Dangote
Shugaban kasa Muhammadu Buhari | Hoto: premiumtimes.ng
Asali: UGC

Marigayi Sani Dangote, ya kasance mataimakin shugaba a rukunin Dangote.

A cikin sanarwar da hadimin Buhari a harkokin yada labarai, Femi Adesina ya fitar ta shafin Facebook, ya bayyana cewa:

Kara karanta wannan

Batun Jaruma Rahama Sadau da wasu sabbin muhimman abubuwa 4 da suka faru a Kannywood

"Shugaban kasan Najeriya Muhammadu Buhari ya mika ta’aziyyarsa ga wanda ya kafa/shugaban rukunin Dangote, Aliko Dangote, bisa rasuwar kaninsa kuma mataimakin shugaban rukunin Dangote, Sani Dangote a ranar Lahadi."

Shugaban ya bi sahun mutane da dama da suka jajantawa Dangote da danginsa kan wannan babban rashi da suka yi.

Yayi addu'ar Allah ya jikansa, kana ya ba dangi hakurin rashin marigayi Sani Dangote.

Allah ya yi wa kanin Aliko Dangote rasuwa

A baya kunji cewa, Sani Dangote, mataimakin shugaban rukunin kamfanonin Dangote kuma kanin Alhaji Aliko Dangote ya riga mu gidan gaskiya.

Mista Dangote ya rasu ne a kasar Amurka a ranar Lahadi 14 g watan Nuwamban 2021 bayan fama da rashin lafiya kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Duk da bai kai dan uwansa kudi ba, Sani Dangote yana da hannun jari a bangarorin noma, banki, man fetur da sauransu.

Kara karanta wannan

Dan uwan Hamshakin Attajirin Nahiyar Afirka, Aliko Dangote, ya rigamu gidan gaskiya

Asali: Legit.ng

Online view pixel