Kotu ta daure lauya shekaru 15 bisa laifukan tafka karya a gaban kotu

Kotu ta daure lauya shekaru 15 bisa laifukan tafka karya a gaban kotu

  • Kotu ta daure lauya shekaru 15 a gidan yari bisa laifin gabatar da hujjojin karya da yiwa kotu karya
  • An kuma bashi zabin biyan tarar da ta kai sama da miliyan biyu bayan kama shi da laifuka guda biyu
  • Rahoto ya bayyana yadda aka yi lauyan ya yiwa kotu karya ya kuma kawo wasu batutuwa don rufe batun

Lagos - Mai shari’a Mojisola Dada ta kotun hukunta manyan laifuka da ke zama a Ikeja a jihar Legas ta daure wani lauya Kenneth Ajoku hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan yari tare da zabin biyan tara bisa laifukan karya da kuma kirkirar shaidar karya.

Alkalin kotun ya kama shi da laifuka biyu a cikin wasu tuhume-tuhume biyun da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta fifita a kansa, Tribute Nigeria ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Dakarun Hisbah sun damke karuwai 44, sun kwace kwalaben Barasa 684 a Jigawa

Rahoto ya ce an fara tuhumar Ajoku ne tun a shekarar 2017 lokacin da hukumar EFCC ta samu bayanan sirri game da gungun ‘yan damfara da ke siyar da kadarorin gwamnatin tarayya.

Kotu ta daure lauya shekaru 15 bisa laifukan gabatar da hujjojin karya
Kotu ta daure lauya bisa laifin karya | Hoto: dailytrust.com

Bayan bincike cikin tsanaki, EFCC ta ce an gayyaci Ajoku da tawagarsa zuwa hukumar, amma ya ki zuwa yayin da aka bukaci ganinsa a lokuta daban-daban.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jami’an hukumar sun ziyarci ofishin wanda ake tuhuma, amma ba a same shi ba.

A wani yunkuri na kawo cikas ga binciken, Mista Ajoku ya tunkari alkalin babbar kotun tarayya da ke Ikoyi, Legas, Ibrahim Buba, domin ya rantse da cewa jami’an hukumar sun kama shi tare da tsare shi a ranar 4 ga Mayu, 2017. Ya kuma bukaci a biya shi diyyar Naira miliyan 300.

Kotun dai ta ki amincewa da bukatar ta kuma umarce shi da ya gabatar da kansa domin binciken hukumar EFCC.

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke wa tsohon manajan banki shekaru 8 a gidan yari kan satar N219m a bankin

Daga nan sai ya garzaya zuwa kotun daukaka kara da ke Legas, a wani mataki na dakatar da binciken da hukumar EFCC ke yi masa.

Kotun daukaka kara, itama ta yi watsi da daukaka karar.

Daga nan aka gurfanar da shi a gaban kotu bisa tuhume-tuhume biyu da suka hada da karya da kirkirar shaidun karya, wanda aka ce ya sabawa sashe na 85(1) 86(1) da 88(1) na dokokin laifuka na jihar Legas, 2011.

Ya musanta tuhumar da EFCC ta ke yi masa, sannan aka ci gaba da shari’ar gaba daya.

A yayin shari’ar, lauyan masu shigar da kara, Franklin Ofoma, ya kira shaidu uku tare da gabatar da wasu takardu da kotun ta amince da su a gabanta.

Da take yanke hukunci a ranar Juma’a, 29 ga watan Oktoba, 2021, Ms Dada ta kama shi da laifuka biyu, sannan ta yanke masa hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan yari, tare da zabin tarar Naira miliyan 2.5, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Kotu ta hana Secondus dakatar da gangamin taron PDP na ƙasa

Nnamdi Kanu ya musanta zargin da ake masa a gaban kotu

A wani labarin, The Cable ta ruwaito cewa, an sake gurfanar da Nnamdi Kanu, jagoran kungiyar ‘yan asalin yankin Biyafara (IPOB) a wata babbar kotun tarayya da ke Abuja bisa zargin ta’addanci.

Kwanan nan gwamnatin tarayya ta sake shigar da laifukan da ake tuhumarsa da shi guda bakwai kari a kan laifuka biyar da a baya yake amsa su, wadanda suka hada da aikata cin amanar kasa da ta’addanci.

An fara zaman kotun a ranar Alhamis da karfe 10 na safe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel