Yanzu-Yanzu: Nnamdi Kanu ya musanta zargin da ake masa a gaban kotu

Yanzu-Yanzu: Nnamdi Kanu ya musanta zargin da ake masa a gaban kotu

  • ahoton da muke samu ya bayyana cewa, an gurfanar da Nnamdi Kanu a gaban kotu, an kuma saurari kara
  • Da aka karanto masa laifukansa, Nnamdi Kanu ya musanta dukkan zargin da ake masa a gaban kotu
  • An fara zaman kotun ne tun karfe 10 na safe, yanzu haka dai ana ci gaba da caccaki tsinke kan batun

The Cable ta ruwaito cewa, an sake gurfanar da Nnamdi Kanu, jagoran kungiyar ‘yan asalin yankin Biyafara (IPOB) a wata babbar kotun tarayya da ke Abuja bisa zargin ta’addanci.

Kwanan nan gwamnatin tarayya ta sake shigar da laifukan da ake tuhumarsa da shi guda bakwai kari a kan laifuka biyar da a baya yake amsa su, wadanda suka hada da aikata cin amanar kasa da ta’addanci.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Nnamdi Kanu ya bayyana a gaban kotu, an hana 'yan jarida shiga

Yanzu-Yanzu: Nnamdi Kanu ya musanta zargin da ake masa a gaban kotu
Shugaban 'yan awaren UPOB, Nnamdi Kanu | Hoto: GettyImages
Asali: Getty Images

An fara zaman kotun a ranar Alhamis da karfe 10 na safe.

Lokacin da aka karanta masa laifukan, shugaban IPOB din ya musanta aikata laifin.

A watan Yuni, an kama Kanu a kasashen waje aka kawo shi Najeriya bayan samun beli da guduwa zuwa Burtaniya a 2017.

Tun lokacin da aka kama shi yana tsare a hannun hukumar tsaro ta farin kaya (DSS).

Jami’an DSS, ‘yan sanda, sojoji sun kewaye kotun Abuja a shari’ar Nnamdi Kanu

Jaridar TheCable ta ruwaito cewa, an girke jami’an tsaro da yawa a babbar kotun tarayya da ke Abuja don shari’ar Nnamdi Kanu, jagoran kungiyar ‘yan asalin yankin Biafra ta IPOB.

An ga jami'an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), rundunar sojan Najeriya da jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya suna gadin kowace kofar shiga kotun da titunan da ke shiga ginin kotun.

Kara karanta wannan

Wakilin Birtaniya ya dira kotu domin shari'ar shugaban 'yan awaren IPOB

Ba a bar 'yan jaridar da sunayensu ba sa cikin jerin shirye-shiryen ba a kusa da harabar kotun, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Nnamdi Kanu ya bayyana a gaban kotu, an hana 'yan jarida shiga

Tun farko, Shugaban 'yan awaren IPOB, Nnamdi Kanu, ya gurfana a gaban kotu bayan wasu jami'an hukumar tsaro ta farin kaya sun kawo shi domin fuskantar shari'a.

An shigar da shi zauren kotun ne yayin da aka tsananta tsaro tare da hana manema labarai daukar bidiyo ko hotunansa, jaridar Punch ta wallafa.

Barista Ifeanyi Ejiofor, shugaban lauyoyi masu kare Kanu, ya tabbatar da hakan ga manema labarai. Ya ce wanda ya ke karewa ya na cikin zauren kotun kuma ya bayyana hotunsu tare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel