Dakarun Hisbah sun yi ram da mata masu zaman kansu 44, sun kwace kwalaben Barasa 684 a Jigawa

Dakarun Hisbah sun yi ram da mata masu zaman kansu 44, sun kwace kwalaben Barasa 684 a Jigawa

  • Hukumar Hisbah ta jihar Jigawa ta bayyana samun nasarar cafke karuwai 44 tare da kwace kwalaban barasa sama da 600
  • Kwamandan hukumar na jihar, Ibrahim Dahiru Garki, yace jami'ai sun kame waɗanda ake zargin ne cikin makonni biyu
  • A cewarsa dokar hana sha da kuma kasuwancin miyagun kwayoyi da jihar ta kafa tana nan kuma tana aiki

Jigawa - Aminiya ta rahoto cewa Dakarun hukumar Hisbah sun damƙe mata masu zaman kansu 44, tare da kwace kwalaban Barasa sama da 600 a faɗin jihar Jigawa.

Kwamandan Hisbah na jihar Jigawa, Ibrahim Dahiru Garki, shine ya sanar da haka a ofishinsa, yayin da yake fira da manema labarai.

A cewar kwamandan jami'ai sun samu wannan nasara ne cikin makonni biyu, kuma da taimakon sauran hukumomin tsaro.

Dakarun Hisbah
Dakarun Hisbah sun yi ram da mata masu zaman kansu 44, sun kwace kwalaben Barasa 684 a Jigawa Hoto: aminiya.dailytrust.com
Asali: UGC

Bugu da ƙari Malam Garki ya bayyana cewa jami'ai sun yi wannan kamen ne a garuruwa 17 dake faɗin jihar.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ISWAP sun farmaki asibiti, sun bankawa karfen sabis wuta a Borno

Yadda Hisbah ta samu wannan nasara

A jawabinsa, kwamandan yace:

"Mun yi ram da mata masu zaman kansu 44, kuma mun cafke wasu mutum uku dake sana'ar siyar da barasa, sannan mun kwato katan 57 na barasa a hannun su."

Ya kuma kara da cewa hukumar Hisbah ta miƙa mutanen ga rundunar yan sandan jihar domin gudanar da bincike da ɗaukar matakin doka.

Shin gwamnati na da masaniya?

Kwamandan ya kuma bayyana cewa Hisbah ta gudanar da wannan aikin ne biyo bayan umarnin gwamnatin jihar Jigawa na garƙame wuraren siyar da barasa da wuraren baɗala.

A cewarsa har yanzun dokar haramta sha da kuma sana'ar miyagun kwayoyi na nan tana aiki a faɗin jihar.

Daga ƙarshe, ya roki al'ummar jihar Jigawa da su cigaba da baiwa Hisbah haɗin kai, ta hanyar taimaka musu da bayanai domin kawo ƙarshen masu wannan halayya.

Kara karanta wannan

Mun san ranar da za'a daina sata da garkuwa da mutane a Najeriya, Shugaban hukumar leken asiri

A wani labarin kuma kun ji cewa da safiyar Laraban nan Babban bututun iskar Gas ya fara kwarara cikin Jama'a a jihar Legas

An gano Gas ɗin na fita ne da misalin ƙarfe 8:00 na safe kuma tuni masu kawo agaji daga kamfanin mai NNPC, jami'an kashe wuta na ƙasa da na jihar Legas suka kama hanyar zuwa wurin.

Rahotanni sun bayyana cewa yoyon iskar Gas ɗin na fitowa ne daga bututun dake kai Gas ma'aikatun dake Ikeja, babban birnin jihar Legas.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel