Yanzu-yanzu: Kotu ta hana Secondus dakatar da gangamin taron PDP na ƙasa

Yanzu-yanzu: Kotu ta hana Secondus dakatar da gangamin taron PDP na ƙasa

  • Kotun daukaka kara ta yi fatali da bukatar da Uche Secondus ya shigar na neman a hana yin babban taron PDP na kasa
  • Alkalan kotun sun cimma matsaya daya kan cewa Secondus bai shigar da kararsa kan lokaci ba kuma yana son bata wa shari'a lokaci ne
  • Lauyan Secondus, Tayo Oyetibo, ya ce dama abin da ya fi muhimmanci a garesu shine daukaka karar da suka yi kan dakatar da Secondus

Uche Secondus, dakataccen shugaban jam'iyyar People's Democratic Party, PDP, na ƙasa bai yi nasara ba a yunkurinsa na hana yin gangamin taron jam'iyyar na ƙasa, TVC News ta ruwaito.

Secondus ya garzaya kotun daukaka kara ne inda ya ke ƙalubalantar dakatar da shi da aka yi a matsayin shugaban Jam'iyyar na kasa.

Ya kuma shigar da wata bukatar a gaban kotu yana neman a hana ta yin gangamin taron ta Na kasa da ta shirya yi a ranakun 30 da 31 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Allah Ya yiwa marubucin littafin 'Kulba na barna', Umaru Kasagi, rasuwa

Yanzu-yanzu: Kotu ta hana Secondus dakatar da gangamin taron PDP na ƙasa
Kotu ta hana Secondus dakatar da gangamin taron PDP na ƙasa. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

The Cable ta ruwaito cewa dukkan alkalan kotun karkashin jagorancin Mai Shari'a Haruna Tsammani sun amince da hukuncin ba tare da jayayya ba.

Gabriel Kolawole wanda ya karanto hukuncin ya ce Secondus bai shigar da kararsa a kan lokaci ba kuma hakan saba dokokin kotu ne.

Kotun daukaka karar ta dora masa laifi na kin shigar da kara a lokacin da aka dakatar da shi a mazabarsa da karamar hukumar har sai yanzu.

Hukuncin na nufin babban jam'iyyar adawar za ta ci gaba da shirin gudanar da taron, wanda a lokacin ne za ta zaɓi sabbin shugabanninta na ƙasa a muƙamai daban-daban.

Martanin Lauyan Secondus

Tayo Oyetibo, lauyan Secondus ya ce babban abin da wanda ya ke karewa ke kallubalanta shine dakatar da shi da aka yi a matsayin shugaban PDP na kasa.

Kara karanta wannan

Dan Sarki a Arewa ya shiga jam'iyyar adawa, ya bayyana shirinsa na tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023

Ya ce zai yanke hukunci kan wannan karar sannan zai san ko zai daukaka kara ko akasin haka.

Uche Secondus ya garzaya kotu don hana gangamin taron PDP na ƙasa

Tunda farko, Legit.ng ta kawo muku cewa Tsohon shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), na kasa, Uche Secondus ya bukaci jam'iyyar ta dakatar da shirye-shiryen da ta ke yi don gudanar da gangaminta na kasa, rahoton Daily Trust.

Tuni dai, jam'iyyar ta fara shirye-shiryen gudanar da taron da za a yi a ranakun 30 da 31 ga watan Oktoban 2021.

Amma cikin wasika da ya aike wa jam'iyyar ta hannun lauyansa, Tayo Oyetibo, SAN, Secondus ya bukaci kotu ta hana jam'iyyar yin taron har sai an yanke hukuncin karshe kan daukaka kara da ya yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel