Kotu ta yanke wa tsohon manajan banki shekaru 8 a gidan yari kan satar N219m a bankin

Kotu ta yanke wa tsohon manajan banki shekaru 8 a gidan yari kan satar N219m a bankin

  • Wata babbar kotu da ke zama a Enugu ta yanke wa tsohon manajan wani banki a Enugu, Mr Anidiobi Chukwuka, hukuncin shekaru 8 a gidan gyaran tarbiyya
  • Ana zargin sa da sata tare da yaudara inda bayan gamsuwa da hujjoji, Alkalin kotun, Justice Cryprian Ajah, ya yanke ma sa hukuncin da ya yi daidai da abinda ya aikita
  • An gabatar da shi gaban kotun bisa zargin sa da wawurar N219,000,000 ta kwastoma sannan ya killace kudaden don amfanin sa na yau da kullum

Jihar Enugu - Wata babbar kotu da ke zamanta a jihar Enugu ta yanke wa tsohon manajan wani banki shekaru 8 saboda sata da almundahana.

Jaridar Independent ta ruwaito yadda alkalin kotun, Justice Cyprain Ajah ya yanke wa Mr Anidiobi Chukwuka hukuncin bayan EFCC ta zarge shi da laifuka 32.

Kara karanta wannan

Bincika Gaskiya: Shin hukumar 'yan sanda ta dawo da Abba Kyari bakin aiki bayan bincike?

Kotu ta yanke wa tsohon manajan banki shekaru 8 a gidan yari kan satar N219m a bankin
Kotu ta yanke wa tsohon manajan banki shekaru 8 a gidan yari kan satar N219m. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

An gabatar da manajan bankin gaban kotu bisa ruwayar The Punch bayan zargin sa da sata da mayar da kudin wani na amfanin sa.

An samu bayanai akan yadda ya yashe N219,000,000 daga asusun wani kwastoma bayan ya adana kudin a bankin.

Lauyan mai kara, Mr Olu Omotayo, ya sanar da manema labarai bayan kammala hukuncin cewa Chukwuka ya aikata laifin ne a ranar 15 ga watan Augustan 2014 da 16 ga watan Nuwamban 2017.

EFCC ce ta gabatar da karar gaban alkali

Omotayo ya ce wanda aka yi wa satar ne ya kai karar Chukwuka gaban EFCC, kuma ya yi hakan ne ta hanyar gabatar da takarda a watan Janairun 2018.

Ya kara da cewa hukumar, reshen jihar Enugu ta yi gaggawar bincike akan lamarin bayan shugaban hukumar ya duba takardar wacce lauyan mai kara ya rubuta a ranar 4 ga watan Yulin 2018 a maimakon sa.

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke wa tireda ɗaurin zaman gidan yari saboda satar akuya a Jos

A cewarsa:

“Bayan EFCC ta kammala binciken ta, daga nan ta gabatar da korafi 32 a kan sa. Ciki har da yaudara, sata, damfara, almundahana da amfani da sunan wani a gaban Alkali Ajah a ranar 7 ga watan Mayun 2019.”

Alkalin kotun ya yanke ma sa hukuncin bayan an gabatar da duk wasu hujjoji gamsassu akan sa.

Kotu ta ɗaure wani matashi da ya yi asubanci ya tafi coci ya sace kujerun roba

A wani rahoton, wata kotun majistare ta daure wani matashi, Lekan Alaka, mai shekaru 19, watanni 3 bisa satar kujerun roba masu kimar N91,200 daga cocin Mount Zion Angelican.

‘Yan sandan sun kama Alaka da laifin sata kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Alkali Olajumoke Somefun ya yanke hukunci bisa tabbatar da laifin da ya aikata bisa ruwayar Vanguard.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel