Legas: Rushe wani unguwar musulmai da gwamnati ke shirin yi ya janyo cece-kuce

Legas: Rushe wani unguwar musulmai da gwamnati ke shirin yi ya janyo cece-kuce

  • Cece-kuce ya fara yawaita bayan gwamnatin tarayya ta bayyana kudirin ta na rushe wata anguwar musulmai don gina tashar motar Lotto a kan babban titin Legas zuwa Ibadan
  • ‘Yan wata kungiyar musulunci ta Zumratul Jamiu Mumin Society of Nigeria sun ce kungiyar kiristoci ta Redeemed Christain Church of God (RCCG) ne ta shirya kullin don korar su daga filin su na yankin Pakuro-Lotto
  • Duk da dai gwamnatin Tarayya da RCCG ma sun musanta wannan zargin amma kungiyar ta ce gwamnati ta na son korar su ne don samar wa RCCG sansani kamar yadda kakakin kungiyar musulman, Alfa Quadim Adejare ya ce

Legas - Cece-kuce ya barke bayan gwamnatin tarayya ta bayyana kudirin ta na rushe wata anguwar musulmai don gina tashar motar Lotto a kusa da babban titin Legas zuwa Ibadan bisa ruwayar Daily Trust.

Read also

Tashin Hankali: Babban bututun iskar Gas ya fara kwarara cikin Jama'a a jihar Legas

‘Yan wata kungiyar musulunci ta Zumratul Jamiu Mumun Society of Nigeria sun ce kulle-kullen kungiyar kiristoci ta Redeemed Christain Church of God (RCCG) ne don kwace wurin su da ke yankin Pakuro zuwa Lotto wurin babban titin Legas zuwa ibadan daga musulmai.

Legas: Rushe wani unguwar musulmai da gwamnati ke shirin yi ya janyo cece-kuce
Rushe wani unguwar musulmai da gwamnati ke shirin yi a Legas ya janyo cece-kuce. Hoto: Daily Trust
Source: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daily Trust ta ruwaito yadda daga gwamnati har kungiyar RCCG su ka dade suna musanta wannan zargin.

Kungiyar sun kasance su na rayuwa da harkokin addinin su a kilomita 43 na babban titin Legas zuwa Ibadan, sun zargi gwamnati da kwace wurin don samar wa RCCG sansani.

Kakakin kungiyar musuluncin, Alfa Quasim Adejare, ya gabatar da takardar mallakar wurin yayin da Daily Trust ta kai ma sa ziyara.

Ya bayyana yadda kungiyar musuluncin wurin ta kwashe shekaru ta na zaune lafiya da makwabtan ta ciki har da cocin Deeper Life Bible da RCCG.

Read also

Zaben Anambra: Yan takarar gwamna 9 sun yi kira ga sakin Nnamdi Kanu

A cewarsa:

“Wanda ya kirkiro kungiyar mu, Muhammad Jamiu babban malamin addinin musulunci ne wanda ake girmama wa, kuma manomi ne.
“Ya kasance ya na sa rawani. sannan shi ya fara kawo salon hada karatun boko da na Islama, inda ya koya mana zama da jama’a lafiya lau.
“Yan kungiyar Deeper Life Church wadanda makwabtan mu ne, ‘yan sanda har da ‘yan RCCG sun san mu masu bin doka ne da son zaman lafiya.”

Adejare ya zargi ‘yan kungiyar RCCG da shirya makircin kwace filin don samar mu su da sansani. Ya ce wannan shirin zai janyo a rushe makarantar firamare da sakandaren gwamnati, dakuna 22 na dalibai da sauran wurare.

A cewarsa a cikin daliban akwai marayu, saboda me gwamnati za ta rushe su don biyan bukatar wata kungiyar addini ta daban?

Adejare ya bayyana yadda ‘yan kungiyar RCCG su ka same su a baya inda ta bukaci su ba su filin don su musanya mu su da wani na daban ko a ina ne amma su ka ki amincewa.

Read also

Gwamnan Legas ya kori daraktan kula da gine-gine bayan rugujewar bene mai hawa 22

Ya ce an same su a 2019 inda aka ce za a gina tashar mota a watan Yunin 2019, amma a watan Fabrairun 2020 sai batun ya canja inda aka ce za a gina sansanin RCCG a wurin.

Dalibai da dama za su rasa matsugunni

Sakataren kungiyar musuluncin, Ahmed Sulaiman Atanda ya ce matsawar aka rushe wurin, daliban sunza su rasa matsugunni.

Har ila yau wata dalibar makarantar sakandaren ta larabci ta Zumratul Jamiu Mumin Aglo, ta ce rushe wurin zai lalata karatun daliban.

Abdul Azeez Aishat ta roki ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Raji Fashola da kada ya cutar da rayuwar su ta hanyar rushe wurin.

Yayin da Daily Trust ta kai ziyara wurin, ta ga kamfanin gine-gine na Julius Berger sun fara duk wasu shirye-shiryen yin tashar.

Mai kula da gine-ginen ya ce ba anguwar musulman kadai rusau din zai shafa ba

Yayin da aka nemi jin ta bakin mai kula da gine-ginen, Monday Ojugbeli ya ce gwamnati za ta rusa gidajen jama’a, gidajen mayuka da sauran wurare ba anguwar kadai bace abin ya shafa.

Read also

Gwamnatin tarayya ta karbi bashin N8.29 trillion cikin kudin yan fansho dake ajiye a banki

Sannan darektan ayyukan kudu maso yamma wanda ke da alhakin ginin, Injiniya Adedamola Kuti ya ce za ayi ginin ne don taimakaon jama’a.

Kuma ya yi fatali da batun cewa don cutar da wani addini ne za a yi rusau din inda ya ce ba anguwar musulman kadai bane akwai sauran wurare da abin ya shafa.

A cewarsa shirin gwamnatin tarayya ne ba na kungiyar RCCG ba, kuma gwamnati ce ta tsara komai.

2023: CAN ta yi gargaɗi kan tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa da mataimaki masu addini iri ɗaya

A wani rahoton kun ji cewa Shugabancin kungiyar kiristocin Najeriya ta CAN sun ja kunnen jam’iyyun siyasa akan tsayar da ‘yan takarar su duk masu addinai daya a zaben 2023 da ke karatowa.

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito kungiyar ta ce kada duk ‘yan takarar su kasance musulmai ko kuma duk kiristoci don hakan na iya yamutsa siyasa a kasar.

Read also

2023: CAN ta yi gargaɗi kan tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa da mataimaki masu addini iri ɗaya

Shugaban CAN, Dr Samson Ayokunle ya yi wannan jawabin ne yayin da ya jagoranci wata ziyara da su ka kai ofishin mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ovie Omo-Agege a ranar Alhamis.

Source: Legit.ng

Online view pixel