Gwamnan Legas ya kori daraktan kula da gine-gine bayan rugujewar bene mai hawa 22

Gwamnan Legas ya kori daraktan kula da gine-gine bayan rugujewar bene mai hawa 22

  • Gwamnan jihar Legas ya dakatar da babban daraktan hukumar kula da gine-gine na jihar
  • An dakatar dashi ne bayan da wani katafaren ginin bene mai hawa 22 ya ruguje a yankin Ikoyi
  • Gwamnan ya kuma bayyana cewa, gwamnati da hukumomi za su ci gaba da bincike kan hadarin

Legas - Jaridar The Naation ta ruwato cewa, gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu ya dakatar da babban manajan hukumar kula da gine-gine ta jihar Legas (LASBCA) Gbolahan Oki.

Gwamnan ya sha alwashin gano abin da ya faru tare da hukunta wadanda ake tuhuma da hannu a rugujewar bene mai hawa 22 da ya ruguje a Ikoyi ta jihar.

Sanarwar da Kwamishinan Yada Labarai da Dabaru Gbenga Omotoso, ya fitar, ta ce gwamnatin jihar za ta kafa wani kwamiti mai zaman kansa da zai binciki rugujewar ginin na kan titin Gerrard, Ikoyi.

Kara karanta wannan

Ka daina zagin Buhari ka biya albashi da fansho: 'Yan Benue sun caccaki gwamnansu

Da dumi-dumi: Gwamnan Legas ya kori daraktan kula da gine-gine bayan rugujewar bene
Ginin da ya ruguje a Legas | Hoto: thecable.ng
Asali: Facebook

Za a zakulo mambobin kwamitin ne daga Cibiyar Nazarin Gine-gine ta Najeriya (NIA), Cibiyar Tsare-tsare ta Kasa (NITP), Kungiyar Injiniyoyi ta Najeriya (NSE) da sauran kungiyoyin kwararru.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

“Za a binciki abubuwan da suka faru na nesa da kai tsaye tare da bayar da shawarwari kan yadda za a hana afkuwar lamarin nan gaba. Binciken ba ya cikin binciken cikin gida da gwamnati ta riga ta gudanar.”

Ya ce an tura karin kayan aiki da ma’aikata a wurin domin ceton rayuka da dama.

Ya ce:

“Mutane tara - dukansu maza - an ciro su daga cikin ginin da ransu. An kai su asibiti. Abin takaici, an fitar da wasu 14 matattu - da misalin karfe 2 na rana.
“Mista Sanwo-Olu ya mika godiyarsa ga dukkan wadanda suka kai daukin farko da wadanda suka shiga aikin ceto, wadanda suka hada da katafaren kamfanin gine-ginen Julius Berger da Kamfanin Gine-gine na kasar Sin (CCECC) da kuma Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta kasa (NEMA).

Kara karanta wannan

Bayan lashe zabe, sabon shugaban matasan PDP ya magantu kan manufarsa akan APC

Za a kafa teburin taimako don gano wadanda suka makale

Gwamnati ta kuma bayyana cewa, za a kafa teburin taimako don taimakawa dangi su gano 'yan uwansu, Vanguard ta ruwaito.

“Za a kafa teburin taimako wurin domin mutanen da ke neman bayanai game da danginsu da watakila suke cikin lamarin.
"Ana sanar da manema labarai cewa gwamnati za ta fitar da bayanai a duk lokacin da bukatar hakan ta taso don guje wa duk wani rahoto mai tada hankali na abin da ya faru."

Ya ce gwamnati za ta ci gaba da gudanar da gwaje-gwajen a matakai daban-daban domin tabbatar da tasirin ginin da ya ruguje.

Buhari ya shiga jimami, ya mika sakon jaje ga iyalan wadanda bene ya ruguje dasu

A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya mika sakon jaje ga iyalan wadanda rugujewar bene mai hawa 22 ya rutsa dasu a jihar Legas ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Bincika Gaskiya: Shin hukumar 'yan sanda ta dawo da Abba Kyari bakin aiki bayan bincike?

A ranar Litinin 1 ga watan Nuwamba ne wani bene mai hawa 22 ya ruguje, inda mutane suka halaka wasu kuma aka yi nasarar ceto su da munanan raunuka.

Da yake bayyana jimaminsa, Shugaba Buhari ya bayyana bukatar daukar matakin gaggawa wajen ceto rayukan wadanda aka ciro daga cikin ginin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel