Gwamnatin tarayya ta karbi bashin N8.29 trillion cikin kudin yan fansho dake ajiye a banki

Gwamnatin tarayya ta karbi bashin N8.29 trillion cikin kudin yan fansho dake ajiye a banki

  • Binciken Jaridar Leadership ya nuna cewa an gano gwamnatin tarayya na karban bashi daga kudin yan fansho
  • A 2019, gwamnati ta bayyana niyyar aron kudaden don wasu manyan ayyuka irinsu gine-gine
  • Mutane sun bayyana rashin amincewarsu da haka amma da alamun gwamnati ta bi bayan fagge

Abuja - Gwamnatin tarayya ta karbi bashin N8.29 trillion cikin kudin yan fansho N12.9 trillion dake ajiye kawo Agustan 2021.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa duk da rashin amincewan da mutane suka nuna bisa wannan niyya a baya, gwamnati ta bi ta bayan fagge da sunan zuba jari wajen karban kudaden.

Zaku tuna cewa a 2019, majalisar tattalin arzikin Najeriya ta bukaci karban bashin N2 trillion daga kudin fansho don yi wasu manyan ayyuka.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Hukumar EFCC ta damke Obi Cubana a ofishinta dake birnin tarayya Abuja

Amma yan Najeriya suka bayyana cewa sam hakan ba zai yiwu ba.

Gwamnatin tarayya ta karbi bashin N8.29 trillion
Gwamnatin tarayya ta karbi bashin N8.29 trillion cikin kudin yan fansho dake ajiye a banki Hoto: Ministry of Finance
Asali: Facebook

Gwamnatin Buhari na shirin aron kudaden yan Najeriyan dake ajiye a banki

A baya mun kawo muku cewa, gwamnatin tarayya na shirin aron kudaden yan Najeriyan da ke asusun da aka dade ba'a waiwayesu ba, da kuma kudaden masu hannun jarin da aka dade ba'a bibiya ba.

Gwamnatin zata samu daman yin hakan ne bisa dokar kudin 2020 da shugaba Muhammadu Buhari ya rattafa hannu.

Karkashin sashe na 12 na dokar, an bayyana cewa za'a iya aron kudaden masu hannun jarin da ajiyan na mutanen wanda suka kai shekaru 6 ba'a waiwaya ba.

Gwamnati tace duk kudaden da ba'a bibiya ba za'a aika su wani asusun lamuni na musamman mai suna 'Unclaimed Funds Trust Fund'.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: An bindige wani mutum a kotu yayin da ya yi ƙoƙarin tseratar da fursuna

Yanzu gwamnatin na shirin aron wadannan kudaden dake cikin asusun, Thisday ta ruwaito.

Kotu ta hana Gwamnatin Buhari aron kudaden yan Najeriyan dake ajiye a banki

An haramtawa gwamnatin tarayya aron kudin da mutane suka sa hannun jari dake ajiye a banki bayan karar da aka shigar da ita kotu.

Alkali J.O Abdulmalik na babban kotun tarayya dake Abeokuta ya hana gwamnati dabbaka wannan doka kuma ya bayyana cewa kada a yiwa mutane barazana kan kudinsu.

Kungiyar masu hannun jari Palm Wealth ta shigar da gwamnatin Buhari kotu kan wannan abu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel