Tashin Hankali: Babban bututun iskar Gas ya fara kwarara cikin Jama'a a jihar Legas

Tashin Hankali: Babban bututun iskar Gas ya fara kwarara cikin Jama'a a jihar Legas

  • Wani babban bututun gas ya fara fitar da iskar gas da safiyar Laraban nan a yankin Ikeja dake Jihar Legas
  • A halin yanzun dai masu aikin gyara daga kamfanin mai na ƙasa NNPC na kan hanyar zuwa wurin domin shawo kan matsalar
  • Hukumar NEMA ta shawarci mazauna yankin da su ɗauki matakin kare lafiyarsu, kada su kunna wuta a yanzu

Lagos - Dailytrust ta rahoto cewa an samu matsalar kwaranyar iskas Gas daga Bututu a yankin Ikeja jihar Legas, kuma tuni aka shawarci mazauna yankin kada su yi amfani da wuta.

An gano Gas ɗin na fita ne da misalin ƙarfe 8:00 na safiyar ranar Laraba kuma tuni masu kawo agaji daga kamfanin mai NNPC, jami'an kashe wuta na ƙasa da na jihar Legas suka kama hanyar zuwa wurin.

Kara karanta wannan

Shin dagaske kasurgumin dan bindigan da ya addabi Arewa, Dogo Gide, ya mutu? Gaskiyar abinda ya faru

Rahotanni sun bayyana cewa yoyon iskar Gas ɗin na fitowa ne daga bututun dake kai Gas ma'aikatun dake Ikeja, babban birnin jihar Legas.

Iskar Gas
Da Dumi-Dumi: Mutane sun shiga tashin hankali yayin da bututun isakar Gas ya fashe a Legas Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Jami'an yan sanda daga sashin A da B reshen Ikeja, sun mamaye yankin yayin da ake jiran isowar waɗan da zasu shawo kan lamarin, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Wane hali mutane dake zaune a yankin ke ciki?

Shugaban hukumar bada agaji ta ƙasa (NEMA) reshen yankin kudu maso yamma, Ibrahim Farinloye, ya shawarci mutane kada su kunna wuta a wani saƙon WhatsApp da ya tura.

Yace:

"Muna gargaɗin mutanen dake zaune a Computer Village/Underbridge, Awolowo Way da Oba Akran axis, Onifowose Street, Medical Road, kada su kuskura su buɗe shaguna ko kunna wuta."
"Mun samu kiran gaggawa cewa iskar Gasa na kwarara a waɗan nan yankuna. Saboda haka mun ɗauki natakan kariya ga lafiyar mu."

Kara karanta wannan

Sabon Hari: Duk da dauke sabis, Yan bindiga sun sake kai wani mummunan hari a jihar Katsina

A wani labarin kuma Yan bindiga sun zagaye wurin Ibada, sun buɗe wa mutane wuta a jihar Kaduna

Miyagun yan bindiga sun harbe mutum biyu, tare da sace wasu da dama a wani sabon hari da suka kai jihar Kaduna.

Rahoto ya bayyana cewa maharan sun zagaye cocin Baptist a ƙaramar hukumar Chikun, suka buɗe wa masu aikin ibada wuta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel