2023: CAN ta yi gargaɗi kan tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa da mataimaki masu addini iri ɗaya

2023: CAN ta yi gargaɗi kan tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa da mataimaki masu addini iri ɗaya

  • Shugabancin kungiyar kiristocin Najeriya ta ja kunnen jam’iyyu akan tsayar da ‘yan takarar shugabancin kasa masu addini daya a zaben 2023
  • Dr Samson Ayokunle, Shugaban Kungiyar, ne ya bayyana hakan yayin da ya jagoranci kungiyar wurin kai ziyara zuwa ofishin mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ovie Omo-Agege
  • Acewarsa, ba sa bukatar ganin ‘yan takara duk musulmai sun tsaya takara tare, ko kuma duk kiristoci saboda gudun kawo wani rikici sakamakon rashin tsaron da ke kasa

FCT, Abuja - Shugabancin kungiyar kiristocin Najeriya ta CAN sun ja kunnen jam’iyyun siyasa akan tsayar da ‘yan takarar su duk masu addinai daya a zaben 2023 da ke karatowa.

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito kungiyar ta ce kada duk ‘yan takarar su kasance musulmai ko kuma duk kiristoci don hakan na iya yamutsa siyasa a kasar.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Ba a gama rikici da Uche Secondus ba, matan PDP za su tafi kotu

2023: CAN ta ja kunnen jam’iyyun siyasa kan tsayar da ƴan takara masu addinai iri ɗaya a zaɓen da ke ƙaratowa
2023: CAN ta gargadi jam’iyyun siyasa kan tsayar da ƴan takara masu addinai iri ɗaya a zaɓen da ke ƙaratowa. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Shugaban CAN, Dr Samson Ayokunle ya yi wannan jawabin ne yayin da ya jagoranci wata ziyara da su ka kai ofishin mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ovie Omo-Agege a ranar Alhamis.

An samu wannan jawabin a wata takarda mai taken, 2023: 'CAN ta ja kunne akan tsayar da ‘yan takara duk musulmai ko kuma duk kiristoci,’ wacce hadimin shugaban CAN na harkokin yada labarai, Fasto Adebayo Oladeji ya bayyana.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An yanko daidai inda shugaban CAN ya ke cewa:

“Yallabai, dangane da zaben 2023, za mu so ‘yan siyasa irin ku su yi abinda ya dace ba tare da an samu wasu matsaloli ba. Yanzu haka kasar nan ta na cikin rashin tsaro.
“Mu na rokon ku akan batun tsayawa takarar shugaban kasa a tabbatar an samu daidaito ta bangaren addinai. Ba ma son ‘yan takara su kasance duk kiristoci ko kuma duk musulmai.”

Kara karanta wannan

Shugabacin Najeriya a 2023: Jerin kungiyoyi 20 da ke goyon bayan Tinubu a zabe mai zuwa

A cikin takardar Ayokunle ya bayyana rashin jin dadin sa da takaicin sa dangane da yadda tattalin arzikin Najeriya ya ke kara lalacewa.

Ya ce:

“Yallabai, coci ta shiga damuwa akan yadda komai ya tashi a kasa kuma mutane da dama sun dena sana’o’in su. Yanzu ana samun hauhawar rashin ayyukan yi.
“Yayin da mu ke yaba wa kokarin majalisu muna roko akan a tallafa wurin gyara don abubuwa su daidaita. A samar da damar ayyuka a kuma rage haraji musamman ga talakawa.”

Shugaban CAN ya yaba wa gwamnatin tarayya akan yadda ta tsaya tsayin-daka wurin dakatar da yaduwar cutar COVID-19 kuma ya hori mutane akan yin riga-kafin cutar.

Omo-Agege ya nuna farin cikin sa akan ziyarar

The Punch ta rahoto cewa mataimakin shugaban majalisar dattawa a na shi bangaren ya bayyana farincikin sa akan ziyarar da su ka kai ma sa.

Kuma ya bukaci da a dinga samun damar zantawa tsakanin majalisar dattawa da kungiyar CAN.

Kara karanta wannan

Atiku zai iya gyara Najeriya: Gwamna ya bayyana gogewar Atiku da PDP a iya mulki

Har ila yau ya yi godiya akan yadda kungiyar ta ke kokarin ganin ta samar da zaman lafiya da hadin-kai a kasa da jajircewa wurin yaki da annobar cutar COVID-19.

Cikin wadanda su ka kai ziyarar akwai sakataran CAN, Joseph Bade Daramola, shugaban CAN na arewa ta tsakiya, Dr Israel Adelani Akanji, Barista Comfort Chigbue, Bishop Stephen Adegbite da Omonuwa Ogiemudia da sauran su.

Dan takarar gwamna ya sharɓi kuka a bainar jama'a yayin yaƙin neman zaɓe a Anambra

A wani rahoton, dan takarar gwamna na jam'iyyar Zenith Labour Party (ZLP) da za a yi a ranar 6 ga watan Nuwamba, Dr Obiora Okonkwo, ya zubar da hawaye a yayin da ya ziyarci garin Okpoko don kaddamar da aikin titi na miliyoyin naira a ranar Laraba.

Aikin titin zai fara ne daga Ede Road, School Road/Awalite da Ojo street ya tsaya a Owerri road a garin Okpoko a karamar hukumar Ogbaru a jihar ta Anambra, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Babban taro: Jerin sunayen ‘yan takara 27 da PDP ta tantance domin zaben kwamitin ayyuka na kasa na jam'iyyar

Okonkwo ya zubar da hawaye ne a lokacin da ya ga wata mata mai shayarwa mai shekaru 30 wadda ta fada cikin kwata bayan ta kasa bin titin saboda rashin kyawunsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel