'Yan bindiga sun farmaki gidajen malaman makaranta a Abuja, sun sace mataimakin shugaban makarantar

'Yan bindiga sun farmaki gidajen malaman makaranta a Abuja, sun sace mataimakin shugaban makarantar

  • Wasu tsagerun yan bindiga sun kai hari gidajen Malaman makarantar sakandare a Abuja inda suka yi awon gaba da mataimakin shugaban makarantar
  • An tattaro cewa mahara dauke da manyan makamai ne suka kai mamaya gidajen malaman makarantar bayan sun daure jami'in tsaron da ke gadi
  • Sun kuma ta harbi ba kakkautawa kafin suka fasa gidan mataimakin shugaban makarantar

Kwali, Abuja - Wasu yan bindiga sun kai hari gidajen malaman makarantar sakandare na Abuja a yankin Yebu da ke karamar hukumar Kwali, sun sace mataimakin shugaban makarantar, Mohammed Nuhu.

Wani malami da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce masu garkuwa da mutane dauke da manyan makamai ne suka kai mamaya gidajen malaman makarantar, Daily Trust ta rahoto.

'Yan bindiga bindiga sun farmaki gidajen malaman makaranta a Abuja, sun tafka barna
'Yan bindiga bindiga sun farmaki gidajen malaman makaranta a Abuja, sun tafka barna Hoto: Daily Trust
Source: UGC

Ya ce wasu daga cikin tsagerun yan bindigar sun mamaye gidajen malaman, yayin da sauran tawagar suka haura katanga zuwa cikin harabar inda daga nan ne suka fasa gidansa sannan suka yi awon gaba da shi.

Read also

Masu garkuwa da mutane sun sace babban limami da 'ya'yansa 2 a Abuja

Ya ce maharan sun daure jami'in tsaron gidajen kafin suka bude kofar gidan wanda abun ya ritsa da shi ta karfi da yaji.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

"Har ta kai, wasu malaman da ke zama a cikin gidajen sun gaza fitowa saboda yadda ake ta harbi ba kakkautawa."

Shugaban kungiyar malaman Najeriya reshen birnin tarayya, Comrade Stephen Knabayi, ya tabbatar da sace mataimakin shugaban makarantar ga jaridar Daily Trust.

Ya ce lamarin ya afku ne yan kwanaki bayan an sace babban limamin masallacin Juma'a na Yabgoji, Abubakar Abdullahi Gbedako, wanda ya kuma kasance mataimakin shugaban makarantar sakandare, Kwaita, duk a yankin Kwali.

Knabayi ya ce kungiyar ta aika sakonnin email da dama zuwa ga hukumar birnin tarayya da shugabannin wasu yankuna domin yin korafi a kan yawan sace-sacen mambobinta.

Da aka tuntube ta, mai magana da yawun yan sandan birnin tarayya, DSP Adeh Josephine, ta ce tana cikin wata ganawa amma za ta kira bayan kammalawa.

Read also

Kaduna: Duk da datse layikan sadarwa, 'yan bindiga sun sace mutum 9, sun bukaci N50m

Mutane shida aka sace a jami’ar Abuja – Hukumar ‘yan sanda

A gefe guda, mun kawo a baya cewa hukumar 'yan sandan babbar birnin tarayya ta tabbatar da cewar 'yan bindiga sun yi awon gaba da akalla ma'aikatan jami'ar Abuja su shida, rahoton Daily Trust.

Da farko Legit Hausa ta kawo cewa wasu tsagerun yan bindiga sun kai hari gidajen Malaman jami'ar Abuja (UniAbuja) cikin daren Talata, 2 ga watan Nuwamba 2021 kuma sun yi awon gaba da mutane.

Mun tattaro cewa yan bindiga sun dira gidajen ne dake unguwar Giri, hanyar zuwa tashar jirgin sama Gwagwalada, Abuja.

Source: Legit.ng

Online view pixel