Mutane shida aka sace a jami’ar Abuja – Hukumar ‘yan sanda

Mutane shida aka sace a jami’ar Abuja – Hukumar ‘yan sanda

  • Rundunar 'yan sandan Abuja ta tabbatar da cewar 'yan bindiga sun sace wasu ma'aikatan jami'ar Abuja su shida
  • Kwamishinan yan sandan birnin tarayya, Babaji Sunday ne ya tabbatar da hakan, inda yace an tura karin tsaro na yan sanda da sojoji zuwa harabar jami'ar
  • CP Sunday ya kuma bayar da tabbacin cewa za a kama miyagun sannan a hukunta su

Gwagwalada, Abuja - Hukumar 'yan sandan babbar birnin tarayya ta tabbatar da cewar 'yan bindiga sun yi awon gaba da akalla ma'aikatan jami'ar Abuja su shida, rahoton Daily Trust.

Da farko Legit Hausa ta kawo cewa wasu tsagerun yan bindiga sun kai hari gidajen Malaman jami'ar Abuja (UniAbuja) cikin daren Talata, 2 ga watan Nuwamba 2021 kuma sun yi awon gaba da mutane.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Yan bindiga sun kai hari Jami'ar Abuja SQ, sun kwashe ma'aikata da 'yayansu

Mutane shida aka sace a jami’ar Abuja – Hukumar ‘yan sanda
Mutane shida aka sace a jami’ar Abuja – Hukumar ‘yan sanda Hoto: University of Abuja
Asali: Facebook

Mun tattaro cewa yan bindiga sun dira gidajen ne dake unguwar Giri, hanyar zuwa tashar jirgin sama Gwagwalada, Abuja.

A cikin wata sanarwa, kwamishinan yan sandan birnin tarayya, Babaji Sunday, ya ce ya tura karin kayan aiki na yan sanda zuwa harabar jami'ar ta Abuja, rahoton Premium Times.

Ya kuma bayyana cewa ya umurci jami’an da su kula da bangaren kwanan ma’aikata da sauran bangarorin jami’ar, domin karfafa tsaro, inganta lafiyar jama’a da kuma kare jama’a a ciki da kewayen jami’ar.

Kwamishinan ya sandan ya kuma bayyana cewa an yi gaggawan tura tawagar hadin gwiwa na 'yan sanda da jami'an soji na bataliya 176 zuwa yankin domin ba jama'a kariya.

Ya ce:

"Binciken farko ya nuna cewa miyagun sun sace mutane shida zuwa daji a lokacin da suka hango jami'an tsaro."

Kara karanta wannan

A yi wa yan bindiga Afuwa kuma a ware kuɗaɗen ɗaukar nauyinsu, Sheikh Gumi ya magantu

Yayin da yake kira ga jama'a da su kwantar da hankalinsu, kwamishinan ya jadadda cewa tuni rundunonin tsaro suka shiga aiki tare da mazauna yankin da nufin ceto wadanda lamarin ya cika da su.

Ya kuma bayar da tabbacin cewa za a kama miyagun sannan a hukunta su.

Yan bindiga sun kai hari Jami'ar Abuja SQ, sun kwashe ma'aikata da 'yayansu

A baya mun kawo cewa, a hirar da Legit Hausa tayi da wata Farfesa, ta bayyana mana cewa lallai an yi awon gaba da abokan aikinsu.

Dan wani Farfesa a tsangayar Lissafi, Yinka Rafiu, ya bayyana ma wakilin Legit cewa Farfesa daya aka sace tare da yaransa.

A cewarsa, da farko an sace matarsa amma daga baya aka sake ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel