Kaduna: Duk da datse layikan sadarwa, 'yan bindiga sun sace mutum 9, sun bukaci N50m

Kaduna: Duk da datse layikan sadarwa, 'yan bindiga sun sace mutum 9, sun bukaci N50m

  • Miyagun 'yan bindiga sun kai farmaki karamar hukumar Kachia ta jihar Kaduna sun sace mutum 9 a kauyen Dangilmi
  • Wannan lamarin na zuwa ne bayan datse layikan sadarwa kuma miyagun sun bukaci miliyan 50 na fansa
  • Shugaban CAN na reshen jihar Kaduna, Rabaren Hayab ya tabbatar da aukuwar lamarin kuma ya ce suna iyakar kokarinsu

Kaduna - Wasu miyagu da ake zargin 'yan bindiga ne sun sace mutum tara daga kauyen Dangilmi wanda ke karkashin karamar hukumar Kachia da ke jihar Kaduna, Daily Trust ta wallafa.

Daily Trust ta tattaro cewa, lamarin ya faru wurin karfe biyar zuwa shida kusa da Jakaranda wuri da ke da nisan mita dari biyar daga makarantan Bethel da aka sace dalibai 121 a ranar 5 ga watan Yuli.

Kaduna: Duk da datse layikan sadarwa, 'yan bindiga sun sace mutum 9, sun bukaci N50
Kaduna: Duk da datse layikan sadarwa, 'yan bindiga sun sace mutum 9, sun bukaci N50. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN, reshen jihar Kaduna, Rabaren John Hayab ya tabbatar da aukuwar lamarin inda yace 'yan bindigan sun kira tare da bukatar kudin fansa har naira miliyan hamsin.

Kara karanta wannan

Dogo Giɗe, hatsabibi shugaban ƴan bindiga ya haramta shan giya da kayan maye a wasu ƙauyukan Zamfara

An tattaro cewa, wannan satar mutanen ta biyo bayan ne duk da datse layikan sadarwa a yanki da sassan jihar, Daily Trust ta wallafa.

"An sace su kusa da jakaranda kuma 'yan bindigan na bukatar miliyan hamsin. Sun kira jiya Juma'a kuma na samu kira daga 'yan kauyen da kuma shugabansu. Na sanar da su abinda za mu iya yi a wannan halin.
"Toh a yau Asabar, dole ta sa na kira shugabannin majami'u da hukumar makarantar kan cewa kada su sake zuwa ko farfajiyar makarantar a yanzu. Wannan matakin mun dauka ne saboda kada mu zama tamkar sakarkaru idan suka sake zuwa sukasace wasu," yace.

Tashin hankali: ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da yaya da kanwarta

A wani labari na daban, Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace wasu kananan yara biyu daga motar iyayensu a Akure, babban birnin jihar Ondo.

Kara karanta wannan

Kogi: 'Yan bindiga sun sheke rayuka 6, sun babbaka fadar Sarki da wasu gidaje masu yawa

Channels TV ta rahoto cewa lamarin ya afku ne da misalin karfe 8:00 na dare a yankin Leo da ke birnin, a ranar Juma'a, 22 ga watan Oktoba.

Maharan sun kai hari ne a mashigin gidan lokacin da mahaifiyar yaran ke bude kofa domin shiga harabar gidansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel