Masu garkuwa da mutane sun sace babban limami da 'ya'yansa 2 a Abuja

Masu garkuwa da mutane sun sace babban limami da 'ya'yansa 2 a Abuja

  • Miyagu sun dira gidan babban limamin Yangoji da ke Kwali a Abuja, sun sace Liman Abdullahi Abubakar Gbedako
  • Sun tsinkayi gidan wurin karfe 11:47 na yamma inda suka dinga harbi tare da hadawa da 'ya'yan limamin biyu suka yi gaba da su
  • Wani daga cikin iyalan limamin, ya tabbatar da cewa miyagun sun kira tare da bukatar kudin fansa har N10 miliyan

FCT, Abuja - Babban limamin masallacin Yangoji da ke yankin Kwali a Abuja, Abdullahi Abubakar Gbedako mai shekaru 59 tare da 'ya'yansa biyu, Aliyu Usman Abubakar mai shekaru 22 da Ibrahim Abubakar mai shekaru 11 sun shiga hannun masu garkuwa da mutane.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, wani makwabcinsu mai suna Shuaibu, ya ce lamarin ya auku a daren Juma'a wurin karfe 11:47 na yamma yayin da aka sace shi. Sun bayyana da yawansu dauke da makamai sannan suka kutsa gidan babban limamin.

Kara karanta wannan

Ba ni da hannu a dirar mikiya da jami'an tsaro suka yi a gidan Mary Odili, Malami

Masu garkuwa da mutane sun sace babban limami da 'ya'yansa 2 a Abuja
Masu garkuwa da mutane sun sace babban limami da 'ya'yansa 2 a Abuja. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ya ce wasu daga cikin 'yan bindigan sun tsaya a wurare daban-daban inda suka dinga harbi a iska yayin da wasu uku suka tsallake katangar gidan limamin.

"Sun dinga harbi tare da lalata kofofin gaban gidan kafin su shiga ciki inda dakin babban limamin ya ke tare da yin awon gaba da shi da 'ya'yansa biyu," yace.

Ya ce an dinga jin harbin bindigan da masu garkuwa da mutanen ke yi a farfajiyar gidan na kusan mintoci talatin kafin su bar gidan, Daily Trust ta wallafa.

Wani dan gidan babban limamin wanda ya bukaci a boye sunansa, ya bayyana cewa an kira su kuma masu garkuwa da mutanen sun bukaci kudin fansa har naira miliyan goma.

A yayin da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar 'yan sandan tarayya, DSP Adeh Josephine, ta tabbatar da satar limamin da 'ya'yansa.

Kara karanta wannan

Kogi: 'Yan bindiga sun sheke rayuka 6, sun babbaka fadar Sarki da wasu gidaje masu yawa

Ta ce yayin da ake cigaba da bincike, 'yan sanda da 'yan sa kai na kokarin ganin sun ceto su.

"Kwamishinan 'yan sandan FCT, CP Sunday Babaji, ya yi kira ga jama'ar Yangoji da su kwantar da hankalinsu tare da samar da bayanan da za su taimaka wa 'yan sanda wurin cafke wadanda ake zargi," tace.

Kaduna: Duk da datse layikan sadarwa, 'yan bindiga sun sace mutum 9, sun bukaci N50m

A wani labari na daban, wasu miyagu da ake zargin 'yan bindiga ne sun sace mutum tara daga kauyen Dangilmi wanda ke karkashin karamar hukumar Kachia da ke jihar Kaduna, Daily Trust ta wallafa.

Daily Trust ta tattaro cewa, lamarin ya faru wurin karfe biyar zuwa shida kusa da Jakaranda wuri da ke da nisan mita dari biyar daga makarantan Bethel da aka sace dalibai 121 a ranar 5 ga watan Yuli.

Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN, reshen jihar Kaduna, Rabaren John Hayab ya tabbatar da aukuwar lamarin inda yace 'yan bindigan sun kira tare da bukatar kudin fansa har naira miliyan hamsin.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun mamaye gidan rasuwa, sun sace bakin da suka halarci jana’iza

Asali: Legit.ng

Online view pixel