Jerin tafiye-tafiyen da shugaba Buhari ya yi zuwa kasashen waje a shekarar 2021

Jerin tafiye-tafiyen da shugaba Buhari ya yi zuwa kasashen waje a shekarar 2021

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ci gaba da tafiye-tafiyen da yake yi a kasashen waje wadanda suka zama wani muhimmin bangare na diflomasiyyar Najeriya da huldar kasashen duniya.

Ya zuwa yanzu a shekarar 2021, shugaba Buhari ya yi tafiya akalla sau hudu zuwa kasashen waje. Duk da cewa a baya fadar shugaban kasar ta bayyana wadannan tafiye-tafiyen a matsayin masu muhimmaci, ‘yan Najeriya da dama sun ce shugaban zai iya tura wakilai.

Yawancin 'yan kasar na da ra'ayin cewa hakan zai rage kashe kudi da kuma baiwa Buhari karin lokaci domin halartar muhimman batutuwan da suka shafi kasa.

Jerin tafiye-tafiyen da Shugaba Buhari ya yi zuwa kasashen waje a shekarar 2021
Shugaba Buhari zai shiga jirgi | Hoto: bbc.com
Source: UGC

A duk lokacin da Buhari ya yi irin wadannan tafiye-tafiye, yakan tafi tare da rakiyar jami’an gwamnati da suka hada da masu daukar hoto, jami’an tsaro, da mataimakansa a harkokin yada labarai daban-daban.

Read also

'Yan Najeriya sun manta Allah: Buhari ya bayyana mafita ga matsalolin Najeriya

Legit.ng ta kawo muku jerin tafiye-tafiyen da shugaban kasar ya yi zuwa kasashen duniya a shekarar 2021.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

1. Kasar Birtaniya

A ranar 30 ga watan Maris ne shugaba Buhari ya tashi zuwa birnin Landan domin duba lafiyarsa kuma ya dawo mako na biyu na watan Afrilu.

Wannan ita ce ziyarar jinya ta farko da shugaban na Najeriya ya kai kasar waje tun bayan barkewar cutar Korona.

A watan Yuli, shugaban ya sake tafiya Landan, wannan lokacin don halartar taron koli na Ilimi na Duniya na GPE 2021-2025.

Bayan kammala taron ilimi Buhari ya shafe lokaci a Landan domin duba lafiyarsa. Ya dawo mako na biyu na watan Agusta.

2. Kasar Amurka

A watan Satumba, shugaba Buhari ya halarci taro na 76 na Majalisar Dinkin Duniya (UNGA76).

Ya yi jawabi ga shugabannin kasashen duniya a ranar Juma’a, 24 ga watan Satumba, inda ya yi jawabi kan taken taro da sauran batutuwan duniya.

Read also

Shugabacin Najeriya a 2023: Jerin kungiyoyi 20 da ke goyon bayan Tinubu a zabe mai zuwa

3. Kasar Habasha

A farkon watan Oktoba shugaba Buhari ya je kasar Habasha inda ya halarci bikin rantsar da Firayim Minista, Abiy Ahmed.

Buhari wanda ya bar Abuja zuwa babban birnin kasar Habasha a ranar Lahadi, 3 ga watan Oktoba, ya shafe kwanaki uku a kasar dake gabashin Afrika.

4. Kasar Saudiyya

A ranar Litinin, 25 ga watan Oktoba, shugaba Buhari ya tafi kasar Saudiyya, domin halartar taron zuba hannun jari da kuma aikin Umarah.

Shugaba Buhari ya dawo daga Saudiyya gabannin taron zuba jari

A wani labarin, Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya dira a birnin tarayya Abuja da yammacin Juma'a, 29 ga Oktoba, bayan tafiyar kwana biyar da yayi Kasar Saudiyya.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ta ruwaito cewa Shugaba Buhari da mukarrabansa sun tashi daga filin jirgin Sarki AbdulAzizi dake Jiddah misalin karfe 15:45.

A kwanaki biyar da yayi a Saudiyya, Buhari ya ziyarci Riyadh, Makkah da Madina.

Read also

2023: Mawakin Buhari, Rarara ya yanke shawarar tsayawa takarar majalisar tarayya

Source: Legit.ng

Online view pixel