Matasan Arewa ga Obasanjo: Kai dai ba ka da bakin sukar gwamnatin shugaba Buhari

Matasan Arewa ga Obasanjo: Kai dai ba ka da bakin sukar gwamnatin shugaba Buhari

  • Kungiyar matasan Arewa sun bayyana rashin jin dadinsu ga yadda Obasanjo ya ke sukar gwamnatin Buhari
  • Kungiyar ta bayyana cewa, Obasanjo bai da bakin da zai iya sukar gwamnatin shugaba Buhari duba da halayensa
  • Kungiyar ta ce maganganu irin na Obasanjo ba komai bane face ta da zaune tsaye da kuma dagula lamurra

Abuja - Kungiyar matasan Arewa (NYA) ta ce tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ba shi da halin da'a da har zai iya sukar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Obasanjo dai ya bayyana a wani taro a Abuja ranar Litinin, inda ya ce Buhari ya yi iya bakin kokarinsa da zai iya, kuma tsammanin ya kara yin wani abu kamar zaburar da mataccen doki ne.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya za su fi ganin amfanin Buhari bayan ya sauka daga mulki, Gwamnan arewa

Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo
Matasan Arewa ga Obasanjo: Kai dai ba ka da bakin sukar gwamnatin shugaba Buhari | Hoto: dailytrust.com
Asali: Twitter

Sai dai a wata sanarwa da mataimakin sakataren yada labaran NYA na kasa Mohammed Hussani Bauchi ya fitar, ya ce tara mutane domin sukar Buhari ba daidai bane.

Ya ce hakan zai kara kamari kan yanayin siyasa da rashin tsaro a Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaridar Ripples Nigeria ta ruwaito sanarwar na cewa:

“Niyya da shirin da tsohon shugaban kasa Obasanjo ya yi na shirya wasu kungiyoyin farar hula da sauran masu sukar gwamnatin Buhari domin su kafa kawancen da za su kara dagula yanayin siyasa da rashin tsaro a Najeriya ba sabon abu ba ne domin ya yi irin haka a gwamnatocin baya da dama.”
“Irin wannan mugun nufi da makirci ga kasar nan abu ne sananne.
“Bayanin ayyukansa (Obasanjo) da cin hanci da rashawa sun dade suna hana shi yin magana na halin kirki kan abubuwan da ke faruwa a kasar nan.

Kara karanta wannan

Farin jinin Shugaba Buhari ya yi mummunan sauka bayan hare-hare da kashe-kashe a Arewa

"Duba da wasu daga cikin halayensa na gwamnati yayin da yake kan mulki zai tunatar da wasu daga cikin mu, halayen tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da kuma abin da yake wakilta."

Ku daina sa ran samun wani abin a mulkin Shugaba Buhari – Obasanjo ga mutanen Najeriya

A wani labarin. tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo yace masu sa ran Muhammadu Buhari zai iya yin abin da ya wuce wanda ya yi, su na bata lokacinsu.

Daily Trust ta rahoto Olusegun Obasanjo ya na kamanta wadanda suka ci buri da gwamnatin Buhari da masu bugun mataccen doki domin ya zabura.

Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana wannan ne a wajen wani zama da Global Peace Foundation da Vision Africa suka shirya domin a tattauna batun tsaro.

Sarkin Musulmi, Mai alfarma, Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya yi jawabi a taron, inda ya yi kira ga shugabanni su daina siyasantar da sha’anin tsaro.

Kara karanta wannan

Umahi ga IPOB: Kun yi kadan, ba ku isa hana shugaban kasa ziyartar kudu maso gabas ba

Samson Ayokunle, Dr. Hakeem Baba-Ahmed, Audu Ogbeh da Bitrus Pogu sun tofa albarkacin bakinsu a madadin kungiyoyinsu na CAN, NEF, MBF da ACF.

Asali: Legit.ng

Online view pixel