Da duminsa: Shugaba Buhari da Uwargidarsa sun dawo gida Najeriya

Da duminsa: Shugaba Buhari da Uwargidarsa sun dawo gida Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo Najeriya bayan tafiyar kwanaki uku da yayi kasar Turkiyya tare da uwargidarsa, Hajiya Aisha Buhari.

Mai magana da yawun Shugaban, Malam Garba Shehu, ya bayyana cewa Buhari ya dura Najeriya ne daidai karfe 2:35.

A cewarsa:

“Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo Abuja bayan halartan taron hadin kan Afrika da Turkiyya tsawon kwanaki uku da akayi a Istanbul.“

Asali: Legit.ng

Online view pixel