Da duminsa: Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo daga Dubai

Da duminsa: Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo daga Dubai

  • Bayan kwanaki hudu ana halartan taruka a birnin Dubai, Shugaba Buhari da tawagarsa sun dawo Najeriya
  • Shugaba Muhammadu Buhari ya halarci taron baja kolin EXPO 2020 da ta gudana yanzu haka a birnin Dubai
  • Buhari ya bayyana yadda annobar Korona ta kawo masa cikas wajen yaki da cin hanci da rashawa

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo Najeriya dawo birnin Dubai, hadaddiyar daular Larabawa da bayan kwanaki hudu don halartan taron baja kolin EXPO 2020.

Buhari ya dira filin jirgin Nnamdi Azikwe dake birnin tarayya Abuja ne da yammacin Lahadi, 5 ga watan Disamba, 2021.

Da duminsa: Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo daga Dubai
Da duminsa: Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo daga Dubai
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Annobar Korona ta kawo min cikas wajen yaki da rashawa, Buhari ga Shugabannin duniya a Dubai

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira ga Shugabannin Duniya su hada karfi da karfe wajen fuskantar kalubalen da al'ummar duniya ke fuskanta.

A jawabin da ya gabatar ranar Juma'a, 3 ga Disamba, yayin taro EXPO 2020 dake gudana a Dubai, Shugaban Najeriyan ya bayyana cewa hada kai zai taimaka wajen kawar da annobar Korona a fadin duniya.

Shugaba Buhari ya bayyanawa EXPO cewa Najeriya, kamar sauran kasashen duniya sun illaltu da annobar COVID-19, wanda ya tsananta lamarin tsaro, yaki da rashawa da kuma fadada tattalin arzikin kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel