Abinda shugaba Buhari yake yi domin kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya, Fadar shugaban kasa

Abinda shugaba Buhari yake yi domin kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya, Fadar shugaban kasa

  • A kullum shugaba Buhari sai ya yi maganar mutanen da ake kashewa tare da yi musu addu'a, inji fadar shugaban kasa
  • Malam Garba Shehu, a wata sanarwa da ya fitar, yace shugaba Buhari yana damuwa fiye da tunani kan halin rashin tsaro da ake ciki
  • A cewarsa gwamnatin tarayya na ɗaukar matakai ta kowane bangare wajen magance matsalolin

Abuja - A ranar Lahadi, fadar shugaban ƙasa ta bayyana namijin kokarin da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ke yi wajen kawo karshen matsalar tsaro a faɗin ƙasa.

Kakakin shugaban, Malam Garba Shehu, a wata sanarwa da ya fitar a Facebook dan martani ga rubutun jaridar Dailytrust mai taken, "Rayuwa bata da daraja karkashin mulkin Buhari."

Yace jaridar ta yi kokari wajen gano ainihin tushen matsalar rikicin dake faruwa, wanda ya samu asali daga talauci da kuma rashin aikin yi.

Kara karanta wannan

Yadda Manjo Hamza Al-Mustapha ya tserad da ni daga yi mun fyade, Hadimar Buhari

Shugaba Buhari
Abinda shugaba Buhari yake yi domin kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya, Fadar shugaban kasa Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

A cewarsa batun da ta ɗakko yana da girma kuma ganin haka yasa ofishin shugaban ƙasa ya ga dacewar maida martani a kansa.

Yace:

"Yawaitar karuwar zubar da jini da kashe-kashe a yankin arewacin ƙasar nan ba abu ne da gwamnati zata lamunta ba. Babu wanda yake tantama akan girman matsalar har shi shugaban ƙasa."
"A kowace rana shugaban ƙasa yana magana kan mutanen da abun ya shafa kuma yana musu addu'a. Byan haka, yana kara jaddada wa yan Najeriya baki ɗaya cewa kawo karshen ayyukan yan bindiga shine abinda gwamnatinsa ta sa a gaba."

Ba Najeriya kadai ke fama da irin haka ba

Malam Shehu ya kara da cewa ba Najeriya kaɗai ke fama da irin waɗan nan masifu da matsalolin tsaro ba, kusan duka faɗin Nahiyar Afirka ana fama da matsalar cikin shekarun da suka gabata.

Kara karanta wannan

Zamu share yan bindiga daga doron ƙasa, Shugaba Buhari ya tabbatarwa gwamnan Sokoto

"Mun fahimci bacin ran jaridar da sauran mutanen yankin arewa baki ɗaya, amma ba su kai gwamnatin Buhari shiga damuwa ba.

Me gwamnati take yi a yanzu?

Sanarwan ta kuma zayyano irin matakan da gwamnatin tarayya take ɗauka wajen kawo ƙarshen matsalolin tsaro baki ɗaya.

Daga cikin matakan, tace dakarun soji na matukar kokari ba dare ba rana wajen magance matsalar yan Boko Haram, masu garkuwa, yan awaren IPOB da kuma yan bindiga.

Kazalika sanarwan tace bayan wannan, gwamnati na amfani da tattalin arzikinta wajen samar da ayyukan yi ta hanyar gina manyan ayyukan ƙasa kamar layin dogo.

Daga ƙarshe ta bayyana cewa lokaci ya yi da kowa zai aje siyasa gefe guda, a haɗa karfi da karfe wajen dawo da zaman lafiya a Najeriya.

A wani labarin na daban kuma hadimar Buhari ta bayyana yadda Manjo Hamza Al-Mustapha ya terad da ita daga yi mata fyaɗe

Shugaban hukumar yan Najeriya dake kasashen waje (NIDCOM), Abike Dabiri-Erewa, ta bayyana irin kalubalen da ta shiga ta yadda aka kusa mata fyaɗe lokacin da take aikin jarida.

Kara karanta wannan

Tsaro: Kungiyar Izala ta yi kira da Buhari ya tashi tsaye, jama’a kuma su dage da addu'a

Tsohuwar yar majalisar tarayya ta shaidawa yan jarida su tashi tsaye kuma su ƙarfafa kansu, su rinka gudanar da binciken kwakkwafi kan wani abu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel