Mutum daya ya rasa ransa yayin da ‘yan daba suka kai hari fadar Hakimin Abuja

Mutum daya ya rasa ransa yayin da ‘yan daba suka kai hari fadar Hakimin Abuja

  • Wasu 'yan daba sun kai farmaki fadar hakimin garin Mpape da ke babbar birnin tarayya Abuja
  • Harin ya yi sanadiyar mutuwar wani Abdurrahman Usman wanda shine ya jagoranci 'yan daban
  • An tattaro cewa rikicin ya fara ne sakamakon sabani da ya shiga tsakanin hakimin da wasu talakawansa da suke adawa da shi kan wasu lamura

Mpape, Abuja - Hankula sun tashi a yankin Mpape da ke babbar birnin tarayya Abuja bayan wani hari da aka kai fadar hakimin garin wanda ya yi sanadiyar rasa rai.

Wani lamari makamancin haka ya faru a garin Mpape sakamakon sabani da aka samu tsakanin hakimin da wasu talakawansa da suke adawa da shi kan wasu lamura.

Daily Trust ta rahoto cewa harin baya-bayan nan ya faru ne bayan hakimin, wanda aka dakatar ya yi umurnin rushe wani gini da ba a amfani da shi kusa da fadarsa a ranar Lahadi.

Read also

Sarkin Birnin Gwari ya ce a yanzu 'yan fashi abinci suke nema maimakon kudin fansa

Mutum daya ya rasa ransa yayin da ‘yan daba suka kai hari fadar hakimin Abuja
Mutum daya ya rasa ransa yayin da ‘yan daba suka kai hari fadar hakimin Abuja Hoto: Daily Trust
Source: UGC

Wasu mazauna yankin sun ce hakimin ya yanke hukuncin ne bisa ga fahimtar juna tsakaninsa da wasu ‘yan uwa biyu da suka mallaki ginin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majiyar ta ce:

“Ya gina masu sabbin gidaje biyu a kusa da hanyar Machafa a nan Mpape, a matsayin madadin tsohon ginin nasu, sannan kuma ya baiwa kowannensu N50,000, yayinda suke komawa gidajen kimanin watanni biyu da suka gabata.
“Don haka a ranar Lahadi sai ya yi umurnin rushe tsohon ginin kamar yadda suka amince, amma sai wasu mutane da ake ganin masu biyayya ne ga mukaddashin hakimi suka ki amincewa da hukuncin. Sai suka far ma fadar da misalin karfe 8:00 na daren ranar Laraba.”

An yi zargin cewa mamacin, mai suna Abdul, shine ya jagoranci ‘yan daban wadanda suka fasa gilashin daya daga cikin motocin hakimin da aka ajiye a fadar.

Read also

Bayan matsalar kwanakin baya, Kamfanin Facebook na shirin sauya suna

Majiyar ta kara da cewa:

“Harma ya cire wayan da ke ba fadar wutar lantarki, amma abun bakin ciki sai aka soke shi har lahira."

Rahoton ya kuma kawo cewa a halin yanzu, an zuba jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda, sojoji da DSS domin gadin gidajen biyu wato fadar hakimin da aka dakatar da kuma gidan mukaddashin hakimin.

Da aka tuntube shi, kakakin ‘yan sandan birnin tarayya, DSP Josephine Adeh, ta tabbatar da lamarin.

Ta bayyana sunan mamacin a matsayin Abdurrahman Usman, wanda tace rundunar yan sandan yankin sun kwashe shi zuwa asibitin Maitama bayan lamarin, inda aka tabbatar da mutuwarsa.

Zargin kashe-kashe: Rundunar ‘yan sanda ta yi karin haske kan rikicin iyakar Bauchi da Gombe

A wani labarin, rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta bayyana cewa ba a rasa rai ko daya ba a yayin rikicin da ya wakana tsakanin garuruwan da ke kan iyaka a jihohin Bauchi da Gombe.

Read also

Da Dumi-Dumi: 'Yan bindiga sun harbe sarakuna biyu har lahira a wurin taro

Kakakin ‘yan sandan jihar, Ahmed Wakil ne ya bayyana hakan ga manema labarai a garin Bauchi a ranar Alhamis, 21 ga watan Oktoba.

Hakan martani ne ga rahotannin cewa an yi kashe-kashen rayuka bayan wasu al’ummomin Gombe sun kai farmaki wasu gonaki a karamar hukumar Ganjuwa da ke jihar Bauchi.

Source: Legit.ng

Online view pixel