Sarkin Birnin Gwari ya ce a yanzu 'yan fashi abinci suke nema maimakon kudin fansa

Sarkin Birnin Gwari ya ce a yanzu 'yan fashi abinci suke nema maimakon kudin fansa

  • Sarkin Birnin Gwari, Alhaji Zubairu Jibril Mai Gwari II, ya magantu a kan halin da 'yan bindiga suka tsinci kansu a jihar Kaduna bayan matakan da gwamnatin jihar ta dauka
  • Mai Gwari ya ce a yanzu masu garkuwa da mutane na neman abinci ne daga wadanda suka sace maimakon kudin fansa
  • Ya yaba sosai da matakan dakile matsalar tsaro da Gwamna Nasir El-Rufai ya dauka a fadin jihart

Mai martaba sarkin Birnin Gwari, Alhaji Zubairu Jibril Mai Gwari II, ya jinjinawa matakan da gwamnatin jihar Kaduna ya dauka domin kawo karshen ayyukan masu garkuwa da mutane.

A cewar sarkin, wadannan matakai sun jefa ‘yan bindigar cikin wani yanayi har ta kai yanzu suna neman abinci daga wajen mutanen da suka yi garkuwa da su maimakon kudin fansa.

Kara karanta wannan

Rahoto: 'Yan bindiga sun sace sama da mutane 830 a jihar Kaduna cikin watanni 3

Sarkin Birnin Gwari ya ce a yanzu 'yan fashi abinci suke nema maimakon kudin fansa
Sarkin Birnin Gwari ya ce a yanzu 'yan fashi abinci suke nema maimakon kudin fansa Hoto: BBC Hausa
Asali: UGC

Sashin Hausa na BBC ta rahoto cewa Basaraken ya fadi hakan ne a ranar Laraba, 20 ga watan Oktoba, yayin taron kaddamar da rahoto kan kalubalen tsaro da ma’aikatar cikin gida ta jihar ta gabatar wa Gwamna Nasir El-Rufai.

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Matakan da gwamnati ta dauka na toshe layukan sadarwa da hana mashin da siyar da man fetur a ko’ina ya yi amfani matuka saboda mun gani a wajenmu kuna muna da labarin yadda al’amarin yake a sauran wurare.
“Wadannan matakai sun takura maharan har ta kai idan suka yi garkuwa da mutane sai dai su nemi a ba su abinci amma ba kudi ba. Muna goya ma gwamnati baya sannan muna addu’ar Allah ya kawo mana karshen wannan lamari.”

An tattaro cewa rahoton ya duba hare-haren da suka gudana na ‘yan fashin daji da ba kabilanci tun daga 1 ga watan Yuli zuwa 30 ga watan Satumban 2021.

Kara karanta wannan

‘Yan Najeriya na fama da yunwa, talauci da rashin tsaro – Sheikh Dahiru Bauchi ya koka

Rahoto: 'Yan bindiga sun sace sama da mutane 830 a jihar Kaduna cikin watanni 3

A gefe guda, mun kawo a baya cewa, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya ce an yi garkuwa da mutane 830 a jihar daga watan Yuli zuwa Satumba 2021.

Ya bayyana hakan yayin gabatar da rahoton tsaro na kwata na 3 ga gwamnan jihar, Nasir El’rufai, ranar Laraba 20 ga watan Oktoba.

A rahoton Daily Sun, Aruwan ya kuma ce sojojin sun kashe jimillar 'yan ta'adda 69 a lokacin da suke kai hare-hare a sassa daban-daban na jihar a cikin wannan lokaci da ya ambata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel