Wata sabuwa: Bayan matsalar kwanakin baya, Kamfanin Facebook na shirin sauya suna

Wata sabuwa: Bayan matsalar kwanakin baya, Kamfanin Facebook na shirin sauya suna

  • Wani rahoto ya bayyana cewa, akwai yiyuwar kamfanin Facebook ya sauya sunansa zuwa wani abu
  • Wannan na zuwa ne daga wani rahoton hasashe da kamfanin jaridar fasaha ta Verge ta fitar
  • Rahoton ya bayyana yiyuwar sunan da za a lakaba wa kamfanin na Facebook, tare da bayyana dalili

Wani rahoton The Verge ya bayyana cewa Shugaban Kamfanin Facebook Mark Zuckerberg zai tattauna batun canjin suna yayin taron shekara-shekara na gamayyar kamfanin a ranar 28 ga Oktoba.

Canjin sunan da aka fada a rahoton zai iya faruwa nan kusa yayin da kamfanin ke shirin fadada ayyukansa fiye da kafofin sada zumunta.

Wata sabuwa: Kamfanin Facebook na shirin sauya suna zuwa wani sunan na daban
CEO na kamfanin Facebook, Mark Zuckerberg | Hoto: theverge.com
Asali: Facebook

A martanin, Facebook ya ce ba ya yin sharhi kan "jita-jita ko hasashe" lokacin da Reuters ta tuntube shi.

Kara karanta wannan

Abun bakin ciki: Yadda ‘da ya kashe mahaifinsa a kan gona a jihar Gombe

Rahoton ya kara da cewa sake sunan zai sanya manhajar ta Facebook a matsayin daya daga cikin kayayyaki da yawa a karkashin wani kamfani wanda kuma zai sarrafa sauran kayansa kamar Instagram, WhatsApp, Oculus, da sauran su.

Shirye-shiryen Facebook a nan gaba

Rahoton ya kara da cewa sake sunan zai kuma nuna Facebook kan habaka abin da ake kira 'metaverse', duniyar yanar gizo inda za a iya amfani da na'urori daban-daban don yin balaguro da mu'amala a cikin wani yanayi mai kama da juna.

Tun daga watan Yuli, Zuckerberg yake habaka "metaverse," wanda aka ambata a cikin littafin 'dystopian' shekaru talatin da suka gabata kuma wasu kamfanonin intanet kamar Microsoft suke amfani dashi.

Hakazalika, akwai yiwuwar sauya sunan kamfanin zuwa wani abu da ya shafi kalmar 'Horizon'. Facebook kwanaki ya canza dandamalin wasan VR na shi, wanda aka fi sani da 'Horizon,' zuwa 'Horizon Worlds.'

Kara karanta wannan

Zamfara: A kalla rayuka 12 sun salwanta, 'yan bindiga sun kone motar 'yan sanda

Google shi ma ya taba canza sunansa

Wannan ba shi ne karon farko da wani babban kamfanin fasaha ya canza sunansa ba domin ya tsawaita abubuwan da yake samarwa.

Baya ga kasuwancin bincike da talla, Google ya kirkiri 'Alphabet Inc' a 2015 a matsayin kamfani babba don gudanar da wasu ayyuka daban-daban, gami da rukunin motarsu mara matuki da fasahar kiwon lafiya, har ma da ba da sabis na intanet a wurare masu nisa.

Facebook zai fara daukar mataki kan masu yada abubuwan batanci kan 'yan siyasa

A baya kadan, Shaharraren kamfanin nan na sada zumunta, wato manhajar Facebook, ya sanar da sabbin ka'idojin da ya fitar na gogewa da hana rubutu ko kalaman batanci ga manyan mutane a kan shafukan Facebook.

Wannan na zuwa ne a cikin wata sanarwar da Facebook ta fitar ta hannun Antigone Davis, wacce Legit.ng Hausa ta samo, inda aka bayyana dalla-dalla manufar shigo da sabuwar dokar.

Kara karanta wannan

A tura matasan NYSC faggen yaki da yan bindiga, wanda ba zai je ba a daina biyansa albashi

Kamfanin Facebook ya yi bayanin cewa, manhajarsa kafa ce ta sada zumunta da ke yada kauna da zaman lafiya, don haka ba zai yarda da batanci kan wasu daidaikun mutane ba, wannan ne dalilin daukar matakin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel