Zargin kashe-kashe: Rundunar ‘yan sanda ta yi karin haske kan rikicin iyakar Bauchi da Gombe

Zargin kashe-kashe: Rundunar ‘yan sanda ta yi karin haske kan rikicin iyakar Bauchi da Gombe

  • Rundunar 'yan sandan jihar Bauchi ta yi martani a kan rahoton da ke cewa an kashe mutane a wani rikici tsakanin garuruwan da ke kan iyaka a jihohin Bauchi da Gombe
  • Mai magana da yawun yan sandan jihar, Ahmed Wakil, ya ce babu wanda aka kashe a rikicin sabanin yadda aka rahoto
  • Wakil ya kuma bayyana cewa wasu mutane ne daga Gombe suka kai farmaki wasu gonaki a karamar hukumar Ganjuwa da ke jihar Bauchi sannan suka yi harbe-harbe a iska

BauchiRundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta bayyana cewa ba a rasa rai ko daya ba a yayin rikicin da ya wakana tsakanin garuruwan da ke kan iyaka a jihohin Bauchi da Gombe.

Kara karanta wannan

Sai mun hada kai ne za mu iya cin galaba a kan miyagu – APC kan harin jirgin kasa

Kakakin ‘yan sandan jihar, Ahmed Wakil ne ya bayyana hakan ga manema labarai a garin Bauchi a ranar Alhamis, 21 ga watan Oktoba.

Rundunar ‘yan sanda ta yi karin haske kan rikicin iyakar Bauchi da Gombe
Rundunar ‘yan sanda ta yi karin haske kan rikicin iyakar Bauchi da Gombe Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Hakan martani ne ga rahotannin cewa an yi kashe-kashen rayuka bayan wasu al’ummomin Gombe sun kai farmaki wasu gonaki a karamar hukumar Ganjuwa da ke jihar Bauchi.

Wakil ya yi bayanin cewa maharan sun yi harbe-harbe ne a iska, inda suka kuma lalata gonaki kafin suka bar wajen, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce bisa ga rahoton da rundunar ta samu, ba a kashe kowa ba a harin. Sannan ya ce rundunar ta tura jami’ai zuwa wajen da al’amarin ya afku kuma tuni zaman lafiya ya dawo a yankin.

Ya kuma ce za a gudanar da wani taro tsakanin gwamnonin Bauchi da Gombe, shugabannin garuruwan da abun ya shafa, sarakunan gargajiya da kuma shugabanni daga yankin, domin tattauna mafita da zaman lafiya mai dorewa a tsakanin garuruwan, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Sarkin Birnin Gwari ya ce a yanzu 'yan fashi abinci suke nema maimakon kudin fansa

Rundunar yan sanda ta bankaɗo waɗanda suke da hannu a kisan Sarakuna guda biyu

A wani labari na daban, kwamishinan yan sanda na jihar Imo, Rabiu Hussaini, ya zargi haramtacciyar ƙungiyar IPOB da mayaƙan ESN da kisan sarakuna biyu a jihar Imo.

The Nation ta rahoto cewa wasu yan bindiga sun baɗe wa sarakunan gargajiya wuta a ƙaramar hukumar Njaba jihar Imo, mutum biyu suka mutu, ranar Talata.

Kwamishinan ya faɗi haka ne a wata sanarwa da kakakin yan sandan jihar, Michael Abattam, ya fitar ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel