An kuma, Miyagun yan bindiga sun kutsa fadar Basarake, sun yi awon gaba da shi a jihar Katsina

An kuma, Miyagun yan bindiga sun kutsa fadar Basarake, sun yi awon gaba da shi a jihar Katsina

  • Wasu yan bindiga sun kutsa fadar basaraken garin Banye dake ƙaramar hukumar Charanchi, jihar Katsina, sun yi awon gaba da shi
  • Rahoto ya nuna cewa maharan sun aikata yadda suke so domin katse hanyoyin sadarwa ya shafi garin, babu hanyar neman a kawo ɗauki
  • Kakakin yan sandan jihar, SP Gambo Isah, yace hukumar yan sanda bata da masaniya kan faruwan lamarin

Katsina - Tsagerun yan bindiga sun yi awon gaba da dagacin garin Banye, dake ƙaramar hukumar Charanchi, jihar Katsina.

Dailytrust ta ruwaito cewa maharan sun sace dagaci, Alhaji Bishir Gide Banye, tare da wani mutum ɗaya da ake tsammanin ɗalibin sakandure ne.

Wani mazaunin garin ya tabbatar da cewa maharan ɗauke da makamai sun mamaye garin Banye ranar Jumu'a da daddare.

Read also

Yadda yan bindiga ke sako mutanen da suka kama ba tare da biyan kudin fansa ba a Zamfara

Yan bindiga a Katsina
An kuma, Miyagun yan bindiga sun yi awon gaba da wani Basarake a jihar Katsina Hoto: channelstv.com
Source: UGC

A cewar mutumin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, maharan sun tafi kai tsaye zuwa fadar basaraken, inda suka sace shi tare da wani mutum ɗaya.

Shin datse hanyoyin sadarwa ya shafi Banye?

Duk da cewa Banye na ƙaramar hukumar Charanchi, amma datse hanyoyin sadarwa da aka yi a ƙaramar hukumar Kurfi ya shafe su.

Wannan matakin na datse sabis, ya sanya maharan sun ci karensu babu babbaka domin mazauna garin ba zasu iya sanar da jami'an tsaro ba, a kawo ɗauki.

Wannan shine karo na biyu da yan bindiga suka sace dagaci a yankin, domin a baya an taɓa sace basaraken Barkiya dake karamar hukumar Kurfi, kamar yadda Premium times ta ruwaito.

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

Da aka tuntubi kakakin rundunar yan sanda, reshen jihar Katsina, SP Gambo Isah, yace basu samu rahoto a hedkwatar yan sanda ta jiha ba zuwa yanzun.

Read also

Wani matashi ya hallaka ɗan shekara 50 da ya kama a dakin budurwarsa suna biɗala

Amma ya yi alƙawarin cewa zai bincika domin tabbatar da lamarin sannan ya sanar, amma har zuwa yanzun babu wani bayani daga gare shi.

A wani labarin kuma Kwastam ta kwace jarkoki 1,000 makare da man fetur za'a kaiwa yan bindiga a Katsina

Mukaddashin shugaban NCS reshen Katsina , Wada Chide, yace mutane na amfani da abun hawansu wajen siyo fetur su juye a jarkokin.

Ya kuma yi kira ga mazauna jihar musamman waɗanda ke zaune a kauyukan dake bakin boda su cigaba da kiyaye doka.

Source: Legit

Online view pixel