Wani Mutumi Ya Mutu a Ɗakin Hotel Bayan Ya Shiga da Wata Mace Zasu Ji Dadi

Wani Mutumi Ya Mutu a Ɗakin Hotel Bayan Ya Shiga da Wata Mace Zasu Ji Dadi

  • An gano gawar wani mutumi awanni bayan ya kama ɗakin Otal tare da wata Karuwa don su ji daɗi a jihar Legas
  • Mai magana da yawun hukumar yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, yace sun samu rahoton faruwar lamarin a layin Omidunu
  • Yan sanda ne suka ɓalla Kofar suka taras ya mutu amma ba'a ga macen da suka zo tare ba, yanzu haka ana kan bincike

Lagos - Wani Mutumi da har yanzu ba'a gano cikakken bayanansa ba ya mutu a ɗakin Otal inda aka gano ya kama kuma ya shiga da wata Karuwa domin su ji daɗin juna a jihar Legas.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Mamacin ya je Otal ɗin da ke Lagos Island tare da matar da yammacin ranar Jumu'a kuma an same shi matacce awanni bayan shigarsu.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Jirgin Yakin Rundunar Soji Ya Yi Hatsari a Kan Gidajen Mutane, Da Yawa Sun Mutu

Kakakin yan sandan Legas, Benjamin Hundeyin.
Wani Mutumi Ya Mutu a Ɗakin Hotel Bayan Ya Shiga da Wata Mace Zasu Ji Dadi Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Bayanai sun nuna cewa matar ta yi takanta daga ɗakin bayan ta fahimci cewa mutumin da suka zo tare ya mutu.

Mai magana da yawun hukumar yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, yace abin al'ajabin ya auku ne a Layin Omidunu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace wasu mutane sun kai rahoton Caji Ofis ɗin Adeniji Adele cewa mutumin ya je Otal ɗin da wata mace kuma sun je kwankwas masa domin sanar da shi lokacin da ya biya ya kare.

Hundeyin ya ƙara da cewa wanda ya kai ƙorafin ya faɗa wa yan sanda cewa sun buga Ƙofar dakin lokuta da dama amma shiru babu wanda ya amsa daga ciki.

Wane mataki yan sandan suka ɗauka

"Bayan jin wannan rahoton nan take DPOn caji Ofis din ya haɗa tawaga ya tura su Hotel ɗin da abun ya faru. Da isarsu suka gane cewa an kulle ƙofar daga cikin ɗakin."

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wani Tsohon Ɗan Majalisar Dokoki a Najeriya

"Tawagar yan sandan suka ɓalle kofar da karfin tsiya kawai suka ga gawar mutumin kwance a kan Gado kuma babu wata shaidar rikici a jikinsa."

- Benjamin Hundeyin.

Hudeyin ya ƙara da cewa hukumar 'yan sanda ta kai gawar mutumin IDA dake Yaba domin gudanar da binciken gawa.

A wani labarin kuma Yan Sanda Sun Gayyaci Mutum 5 Kan Mutumin Da Ake Rufe Tsirara Na Fiye Da Shekaru 20 A Kaduna

Yan sanda a Kaduna sun gayyaci mutane biyar domin taimaka musu da bincike kan mutumin da aka gano an rufe a daki.

A ranar Laraba ne rundunar yan sandan suka ceto mutumin a wani gida da ke Bayajida cikin daki da ake ce an rufe shi kimanin shekaru 20.

Asali: Legit.ng

Online view pixel